Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana Gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf a ƙoƙarinsa na kyautata dagantaka tsakanin manoma da makiyaya ya bayar da dama ga dukkanin shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano su taimaki Fulani akan labi da makiyaya don kyautata sha’anin rayuwar Fulani.
Babbar mataimakiya ta musamman ga Gwamnan Kano akan Fulfulde Hajiya Rukayya Umar Gadon ƙaya ce ta bayyana hakan a taron ƙungiyar sulluɓawa da aka yi a Kano ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya tsaf yana da kyawawan ƙudure-ƙudure domin bunƙasa cigaban Fulani da za a gamsu a aikace ana aiwatar da su.
Ta ce yanzu haka lura da yadda Fulani ke shan wahala a zuwa aikin Hajji ya shirya ɗaukar malamai da za su yara Fulatanci su jagoranci Fulani wajen aiwatar da ibadar aikin Hajji .Sannan zai ɗauki ‘ya’yan Fulani waɗanda suka san harkar lafiya su riƙa kula da harkar magani duk irin waɗannan tsare-tsare da yawa suna nan tafe.
Hajiya Ruƙayya Umar Gadon ƙaya ta ja hankalin Fulani musamman makiyaya da manoma da cewa su sani abinda ya yi manomi shine ya yi makiyayi, tamkar ɗanjuma da ɗanjummai suke, domin mai kiwon shanu yana noma yaci abinci ,manomi shima yana buƙata daga makiyaya akwai auratayya a tsakani ya kamata a yi wa juna adalci.
Ta ce ka da Fulani su riƙa tura yara ƙanana suna yi wa manoma ɓarna a gonaki su tura masu hankali suma masu noma in suka kwashe abinda suka noma sai su barwa makiyaya su ɗan kalaci abincin shanu kada a riƙa binsu da sara da duka har a tunzura su, abu ya riƙa zama rigima a tsakani, hakan ba daidai bane domin zaman lafiya ya fi komai a rayuwa.
Hajiya Ruƙayya Umar Gadon ƙaya Babbar mataimakiya ta musamman ga Gwamnan jihar Kano akan Fulfulde ta yi fatan Allah ya haɗa kan Fulani da manoma kuma su gujewa fushi da ɗaukar doka a hannu duk abinda ya taso a je ga hukuma da aka tanadeta domin ƙwatowa kowa ‘yancinsa kuma duk abinda ya taso akai ga magabata don ɗaukar mataki.
