Gwamnan Gombe ya ba iyalan ‘yan jarida bakwai da suka rasu a hatsarin mota miliyan N14

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Gombe ta gabatar da Naira miliyan 14 ga iyalan ‘yan jaridar nan guda bakwai da suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan jaridar sun rasu ne a ranar Litinin yayin komawa gida daga bikin wani abokin aikinsu da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kaltungo da ke jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatinsa, Farfesa Abubakar Njodi ne ya gabatar da tallafin miliyan N2 ga kowane iyalan da iftila’in ya shafa a Gombe, ranar Juma’a.

Njodi ya bayyana cewa, an ɗauki matakin bada tallafin ga iyalan ne domin rage musu raɗaɗin rashin da ya same su da kuma taimaka musu wajen rage kashe-kashen kuɗaɗen jana’iza.

Ya kuma bayyana rashin a matsayin babban al’amari duba da yadda waɗanda ya shafa sun kasance daga cikin masu hidimta wa gwamnatin jihar.

Farfesan ya ƙara da cewa, gwamnatinsu tana tare da makusantan mamatam musamman gidan talabijin na NTA, wanda galibin waɗanda al’amarin ya rutsa da su ma’aikatansa ne.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa (NUJ), Alhassan Yahya, ya yi godiya ga gwamnatin bisa tallafin da take bayarwa tun farkon faruwar al’amarin.

Sannan, ya ce NUJ za ta ƙaddamar da shirin inshorar lafiya da walwalar ‘yan jarida a faɗin Nijeriya domin ƙarfafa wa harkokinsu.

By ukarofi