INEC ta musanta fitar da jaddawalin zaɓen 2027

Spread the love


Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa ta fitar da jaddawali da tsarin ayyukan babban zaɓen 2027.

A sanarwar da hukumar ta fitar a jiya Juma’a ta hannun Sakataren labarai kuma mai ba Shugaban INEC shawara akan lamuran yaɗa labarai, Adedayo Oketola, hukumar ta ce rahoton ba gaskiya ba ne kuma abu ne aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.

Inevitable ta jaddada cewa, ba ta fitar da kowane jaddawali ko tsarin ayyuka dangane da babban zaben 2027 ba zuwa yanzu.

Ta ce, tana aiki ne bisa tanadin doka, musamman sashe na 28(1) na Dokar Zaɓe ta 2022, wadda ta tanadi cewa dole ne hukumar ta wallafa sanarwar zabe aƙalla kwana 360 kafin ranar da aka kayyaɗe domin gudanar da babban zaɓe.

Saboda haka ne ta ce duk wani jaddawalin ko tsari da aka fitar a waje da wannan tanadi ba zai taɓa fitowa daga bakin hukumar ba.

Haka kuma, ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za ta fitar da sahihin jadawali da tsarin ayyukan babban zaɓen 2027 a lokacin da ya dace wajen bin ƙa’idojin Kundin Tsarin Mulki na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) da kuma Dokar Zaɓe ta 2022.

A ƙarshe, INEC ta ce idan lokacin ya yi za ta sanar da jama’a ta hanyoyin sadarwar da ta amince da su a hukumance, tana mai kira a gare su da su ƙaurace wa rahoton na ƙaryar.

By ukarofi