Majalisar Dokoki ta fitar da bayanan sabuwar dokar haraji ga jama’a don nazari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da sabuwar dokar haraji a Nijeriya, Majalisar Dokoki ta fitar da kwafin bayanan da dokokin suka ƙunsa don amfanin masu buƙata acikin al’umma da ɓangarorin haɗaka.

A ranar Alhamis ne Akawon majalisar, Barista Kamoru Ogunlana ya sanar da haka ta wata takarda da Daraktan yaɗa labarai, Bullah Audu Bi-Allah ya fitar.

Ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne sakamakon kiraye-kirayen wasu daga cikin ƴan Nijeriya da ke neman yadda za a tantance sahihancin saƙonnin da ake yaɗawa game da sabuwar dokar harajin.

Ogunlana ya ce, hakan zai ba al’umma damar yin nazarin takardun da kuma tantance saƙonnin da ke cikinsu.

Ya kuma ce, ana tsammanin wallafa su a ranar 1 ga watan Junairu, 2026 ko kafin haka ta yadda al’umma za su same su cikin sauƙi tare da gano haƙiƙanin abin da dokar ta ƙunsa.

Wannan na nuni da cewa fitar da kwafin takardun ya ta’allaƙa ne da maɗaba’ar wallafa ta gwamnatin tarayya, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

By ukarofi