Wasu jihohin na shirin karɓar bashin tiriliyoyin Naira don cike kasafin 2026

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Aƙalla jihohi goma a Nujeriya na shirin tara kimanin naira tiriliyan 4.287 ta hanyar karɓar bashin banki, fitar da takardun bashi, tallafi, kuɗaɗen shiga na musamman da kuma haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu, domin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da ke cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Wannan na nuna ƙaruwar matsin lambar kuɗi da ke fuskantar gwamnatocin jihohi.

Rahoton News Point Nigeria ya nuna cewa jihohin Legas, Abia, Ogun, Enugu, Osun, Delta, Sakkwato, Edo, Bayelsa da Gombe sun gabatar da jimillar kasafin kuɗi naira tiriliyan 14.174 ga majalisun dokokinsu, kamar yadda nazarin takardun kasafin kuɗi ya bayyana.

Binciken ya nuna cewa duk da dogaro da kuɗazen rabon FAAC, kuɗin harajin ɓAT da kuma kuɗaɗen shiga na cikin gida, jihohi da dama na ƙara karkata ga hanyoyin samun kuɗi na wucin gadi domin cika burin manyan ayyukan more rayuwa da ci gaba.

Jihar Legas, wadda ita ce cibiyar kasuwanci ta ƙasa kuma ke da mafi girman kasafin kuɗi a tsakanin jihohi, ta gabatar da kasafin kudin naira tiriliyan 4.237 na shekarar 2026. Duk da sa ran samun naira tiriliyan 3.12 daga IGR da kuɗaɗen tarayya, jihar na shirin tara naira tiriliyan 1.117, kimanin kashi 26.4 cikin 100, ta hanyar bashi da takardun bashi domin ɗaukar nauyin manyan ayyukan raya ƙasa. Ko da yake kuɗaɗen shigar Legas na iya yin gogayya da na wasu ƙananan ƙasashen Afirka, karɓar bashi har yanzu muhimmin ɓangare ne na dabarun ci gabanta, musamman a ɓangaren sufuri, gidaje da gine-gine.

Tsohon Shugaban Jami’ar Crescent, Farfesa Sheriffdeen Tella, ya gargadi jihohi da su fi maida hankali kan tanadin kuɗi da habaka hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, maimakon yawan dogaro da bashi. A cewarsa, matsalar kuɗin Nijeriya ba ƙarancinsa ba ce, illa sakaci da lalacewar kuɗaɗen.

A Abia kuwa, kasafin kuɗin naira tiriliyan 1.016 ya bayyana gibin kuɗi da ke fuskantar jihohin da ba su da ƙarfin tattalin arziki sosai. Jihar na sa ran samun naira biliyan 607.2 daga FAAC, ɓAT da tallafi, yayin da gibin naira biliyan 409, kimanin kashi 40.3 cikin 100, za a cike shi ne ta hanyar bashi. Duk da haka, Abia ta samu raguwar bashin cikin gida sosai a 2025, inda ta rage bashinta da kashi 57.2 cikin 100 zuwa naira biliyan 48.6, a cewar Hukumar DMO.

Ogun ta gabatar da kasafin kuɗin naira tiriliyan 1.669, inda take buƙatar naira biliyan 518.9 daga bashi da tallafi duk da samun kudaden IGR da na tarayya. Enugu kuma na shirin karbar naira biliyan 329 domin tallafa wa kasafin kuɗinta da ya ƙaru da sama da kashi 66 cikin 100. A Osun, kusan kashi 40 cikin 100 na kasafin kuɗin ya dogara ne da kudaden wucin gadi, duk da raguwar bashin da aka samu a shekarun baya.

Jihar Delta na fuskantar gibin naira biliyan 694 duk da ƙaruwar IGR, yayin da Gombe ta fi kowa dogaro da bashi, inda sama da kashi 60 cikin 100 na kasafin kudinta zai fito ne daga karbar bashi. A gefe guda kuma, Bayelsa na daga cikin jihohin da suka fi takaita bashi, inda kashi 7.4 kacal na kasafin kuɗinta aka ware daga wannan tushe.

Masana tattalin arziki na gargaɗi cewa dogaro da kuɗaɗen wucin gadi na iya barazana ga ɗorewar kasafin kuɗi a nan gaba, musamman ga jihohin da ke da raunin IGR. Sun jaddada cewa sai an inganta hanyoyin samun kuɗaɗen cikin gida da gaskiya wajen kashe su, kafin a tabbatar da ɗorewar tattalin arzikin jihohi.

By ukarofi