NDLEA ta kama tsohon fursuna da hodar iblis cikin ledar sitaci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wani tsohon fursuna mai suna Nwobodo Chidiebere Basil tare da wasu jami’an dakon kaya uku, bisa zargin yunƙurin fitar da hodar iblis zuwa ƙasar Birtaniya ta hanyar ɓoye ta a cikin kwalayen sitacin ruwa.

NDLEA ta bayyana cewa an gano leda 75 na hodar iblis masu nauyin kilogiram 1.50, da aka ɓoye a cikin jakunkunan sitaci da aka rufe su daga masana’anta, a wajen fitar da kaya na Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed, Ikeja a Jihar Legas.

A wata sanarwa da kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, ya ce an kama jami’an dakon kaya uku — Jubrin Hassana, Kuku Oluwasegun da Igwe Jane — a ranar Asabar, 20 ga Disamba, 2025, da hannu a wannan lamari.

Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga gano Nwobodo, mai shekaru 37, a matsayin wanda ya shirya wannan safarar. An kama shi washegari, Lahadi 21 ga Disamba, a wani wurin shaƙatawa a Ikeja.

Sanarwar ta ce, Nwobodo sanannen dillalin miyagun ƙwayoyi ne da aka taɓa yanke masa hukunci a shekarar 2023, bayan an kama shi da kilogiram 30.10 na kwayar methamphetamine da aka ɓoye a cikin kwalayen custard ana shirin kai su Landan. Kotun Tarayya ta yanke masa hukuncin shekaru biyar a gidan yari, tare da zaɓin tara na naira miliyan 7, da kuma aikin hidimar al’umma na wata guda. Bayan ya biya tarar, ya koma aikata laifin.

Babafemi ya ce, baya ga wannan kamun, NDLEA ta kama wani direba mai shekaru 65 a Jihar Gombe ɗauke da allurar pentazocine guda 300 da kuma ƙwayoyin tramadol 27,900, yana kan hanyar Gombe zuwa Biu a Jihar Borno. Haka kuma, an kama wani ɗan kasuwa mai suna Ignatius Egbochie (Brown) a Apapa, Legas, bisa alaƙa da kama kilogiram 26 na wiwi mai suna “loud” a tashar jirgin ruwa ta Tincan.

NDLEA ta ce, waɗannan nasarori na daga cikin ci gaban da hukumar ke samu tun bayan naɗa Janar Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin shugaban NDLEA a shekarar 2021, inda aka sake naɗinsa a zamanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

By ukarofi