Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Harkokin Inshora ta ƙasa (NAICOM) ta jaddada matsayinta na cewa ba za ta tsawaita wa’adin sake gina jarin kamfanonin inshora ba, tana mai cewa duk wani kamfani mai tsananin niyya da muhimmanci a harkar, ya kamata ya iya cika sharuɗɗan kafin ranar da aka ƙayyade.
Babban Kwamishinan Inshora na ƙasa, Olusegun Ayo Omosehin, ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida kan inshora a Abuja.
Ya ce wa’adin sake gina jarin, wanda aka sanya zuwa ranar 30 ga Yuli, 2026, ya samo asali ne kai tsaye daga Dokar Gyaran Masana’antar Inshora ta Nijeriya (NIIRA), don haka ba abu ne mai sauƙin sauyawa ba.
Omosehin, wanda Mataimakin Kwamishinan Inshora (Bangaren Fasaha), Dakta Usman J. Jankara, ya wakilta, ya bayyana cewa duk wani yunƙurin tsawaita wa’adin zai tilasta wa hukumar komawa Majalisar Dokoki ta ƙasa domin gyara doka, matakin da NAICOM ba ta da niyyar ɗauka.
A cewarsa, sake gina jarin wajibi ne domin tsaftace masana’antar da kuma tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki sun fi ɗaukar kamfanonin inshora da muhimmanci.
Ya ce sake gina jarin zai ja hankalin sababbin kuɗaɗe zuwa masana’antar, tare da bai wa kamfanonin da ke da ƙarfi damar samar da ayyuka masu amfani ga ‘yan ƙasa. A cewarsa, babban manufar wannan tsari ita ce tilasta wa kamfanoni su ƙara jari, inda kasuwar hannayen jari ke zama daya daga cikin hanyoyi mafi sauƙin tara kuɗaɗe.
NAICOM ta kuma bayyana cewa ta shirya taswira ta musamman domin sauƙaƙa tsarin tara jari, inda Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari (SEC) ta bayar da tabbacin cewa za ta riƙa amincewa da buƙatun tara kuɗaɗe cikin gajeren lokaci, maimakon jiran watanni kamar yadda aka saba a baya. Wannan, a cewar hukumar, zai taimaka wa kamfanonin inshora wajen cika sharuɗɗan da aka gindaya cikin lokaci.
Hukumar ta danganta buƙatar sake gina jarin da tasirin hauhawar farashi da kuma raguwar darajar naira, wanda ya rage ƙimar jarin da aka ƙayyade a baya.
A cewar Omosehin, jarin da aka sanya a shekarar 2007 wanda ya kai biliyan 2 zuwa 5 naira, a wancan lokaci ya kai kusan dala miliyan 20, amma a yau irin wannan kuɗi bai kai dala miliyan biyu ba.
NAICOM ta ce manufarta ba wai kawai ƙara yawan kamfanonin inshora ba ce, illa samar da kamfanoni masu ƙarfi, nagarta da jajircewa, da za su iya tsayawa daram su kuma taimaka wajen gina amincewa da inshora a idon ‘yan Nijeriya.
