Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da soke wani gagarumin kaso na bashin da Asusun Tarayya ke bin Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC), matakin da ya zo bayan kammala tantance bayanai da daidaita alƙalumma tsakanin ɓangarorin biyu.
Matakin ya soke bashin da ya kai kimanin dala biliyan 1.42, daidai da Naira tiriliyan 2.059, tare da wani ƙarin bashin Naira tiriliyan 5.57, wanda gaba ɗaya ya kai Naira tiriliyan 7.58. Wannan na nuni da babban sauyi a kan nauyin bashin da NNPC ke ɗauke da shi ga baitul-malin ƙasa.
Rahotanni sun bayyana cewa an fayyace wannan shawara ne a cikin wata takarda da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur, wato NUPRC, ta gabatar a taron Kwamitin Rabon Asusun Tarayya (FAAC) na watan Nuwamba 2025. Shawarar ta biyo bayan shawarwarin Kwamitin Daidaita Masu Ruwa da Tsaki kan Sasantawa da Tantance Bashin da ke tsakanin NNPC da Tarayya.
Takardar ta nuna cewa soke bashin ya shafi tsofaffin basussuka da aka tara har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2024. Cikin basussukan akwai na yarjejeniyoyin Production Sharing Contracts, nauyin samar da man fetur ga cikin gida, yarjejeniyoyin biyan bashi, tsare-tsaren modified carry, da kuma kuɗazen royalty na haɗin gwiwar Jɓ da PSC.
An bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan aikin sasantawa da NUPRC ta jagoranta, tare da amincewar Kwamitin Masu Ruwa da Tsaki, kuma tuni aka yi gyare-gyaren lissafi a cikin Asusun Tarayya domin nuna sabon matsayi.
Duk da wannan sauƙi da aka bayar kan tsofaffin basussuka, rahoton ya nuna cewa sabbin basussukan shekarar 2025, daga Janairu zuwa Oktoba, har yanzu suna nan a matsayin bashi, kuma hukumomi na ci gaba da bibiyarsu domin tabbatar da karɓo su yadda ya dace.
A gefe guda kuma, har yanzu ana ci gaba da taƙaddamar da ta dade tana gudana game da zargin rashin tura kuɗaɗen shiga da suka kai dala biliyan 42.37 tsakanin shekarun 2011 zuwa 2017. NNPC ya ci gaba da musanta zargin, yana mai jaddada cewa an yi cikakken bayani da lissafin dukkan kuɗaɗen da aka samu a wancan lokaci.
Masana harkokin tattalin arziki na ganin cewa soke wannan bashin na iya rage matsin lamba a kan alaƙar kuɗi tsakanin NNPC da Gwamnatin Tarayya, tare da ba gwamnati damar tsara sabbin tsare-tsare na kuɗaɗen shiga da kashe-kashe cikin sauƙi. Sai dai suna jaddada muhimmancin tabbatar da gaskiya da cikakken bibiya kan sabbin basussuka, domin kauce wa maimaita irin wannan nauyi a nan gaba.
