
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa al’umma cewa aurensa da Zainab Musa Kwankwaso, ‘yar tsohon ubangidansa na siyasa kuma tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙare. Ya bayyana haka ne yayin jawabi ga ‘yan fansho a wani taro da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Kano a ranar Litinin, inda ya yi amfani da habaici wajen sanar da batun.
Da yake jawabi cikin harshen Hausa, gwamnan ya bayyana halin aurensa a matsayin abin da ya samu koma baya, inda ya ce ya tashi daga “kofur” zuwa “kwanstabul”, sakamakon rabuwarsa da matar tasa ta biyu, wadda suka shafe tsawon shekaru 20 suna matsayin mata da miji.
Saidai, Abba Kabir Yusuf ya ce akwai yiwuwar ya sake yin wani auren a nan gaba, yana mai cewa zai kasance mai mata ɗaya na ɗan wani lokaci. “Ina mai shaida muku cewa, zan sake ƙara wata mata. Wasunku ba lallai su fahimci abin da gwamna yake nufi ba a nan,” inji shi.
Ya kuma tabbatar da cewa an riga an kammala aiki kan dukkan ababen da suka shafi sakin, inda ya ce an riga an bayar da takarda. Kazalika, ya roƙi al’umma da su sanya shi a cikin addu’o’insu na fatan ya samu mace ta gari, inda ya ƙara da cewa ya yi farin ciki da matakin kuma yana roƙon Allah ya haɗa shi da mutanen kirki.
Kalaman gwamnan na zuwa ne ƙasa da kwana biyu da wasu rahotannin suka karaɗe kafafen labarai cewa, Zainab Musa Kwankwaso ta shigar da ƙarar neman saki a wata Babbar Kotun Yanki da ke yankin Gudu a Abuja.
Wannan al’amari dai ya haifar da cece-kuce acikin al’umma musamman ganin yadda Abba ya kasance na hannun daman Kwankwaso a harkokin siyasa. Sannan, babu wani saƙo daga ɓangaren iyalan Kwankwaso ko ofishin gwamnan kan musabbabin al’amarin.
