Ɗaruruwan mambobin ADC sun sauya sheƙa zuwa APC a Zango

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗaruruwan mambobin jam’iyyar adawa ta ADC a ƙaramar hukumar Zango sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a yayin gangamin yaƙin neman sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa na 2027, wanda aka gudanar a ƙaramar hukumar.

Jigo a jam’iyyar ADC, kuma Shugaban ƙungiyar G5 a ƙaramar hukumar Zango Alhaji Auwali Inchille tare da Malam Tijjani Zango, ne suka jagoranci ɗaruruwan mambobin ƙungiyar wajen komawa jam’iyyar APC.

Gwamna Raɗɗa ya yi maraba da sabbin mambobin jam’iyyar APC, tare da bayyana jin daɗinsa bisa matakin da suka ɗauka na shiga jam’iyyar, yana mai tabbatar musu da cewa za su samu gurbi da kulawa a cikin tafiyar jam’iyyar.

Ya bayyana wasu daga cikin ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta aiwatar a ƙaramar hukumar Zango, musamman a fannin kiwon lafiya, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa ta samar da asibiti na zamani (General Hospital) domin inganta lafiyar al’umma da sauƙaƙa musu samun kulawar lafiya.

Gwamnan ya ce: “A wannan gari mun zo mun buɗe muku asibiti na zamani,” inda ya bayyana wannan kaɗai ya isa al’ummar ƙaramar hukumar Zango su sake zaɓen Ƴan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027, tunda shugaban ƙasa har zuwa ɗan majalissar jiha.

Gangamin na Zango na cikin jerin rangadin yaƙin neman sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa na 2027 a ƙananan hukumomin shiyyar Daura.

By ukarofi

Leave a Reply