Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D
Shimfiɗa
A kullum kalmar soyayya sauƙin faɗa ne da ita a bakin wanda bai tsinci kansa cikinta ba, kunne kan ɗauki kalmar da kalma mafi arha da ya saba ji ko’ina. Gajiyayyiyar kalma ce da take zagaya wa gida-gida, amma idan ta sarƙi wani a cikin gida sarautarta ta fi ta sarkin gari. Kalma ce mafi sauƙi a ɓangaren wanda bai afka ba, amma wanda ya tsinci kansa ciki ta fi komai tsauri. Zuma ce, a hannu guda kuma masu yin ta sukan kira ta da guba. Abin takaici kuma shine, ba kasafai zazzafan so ya kan yi kyakkyawan ƙarshe ba, saboda yadda ake yanke hukunci a cikinsa ko dai cikin son rai ko cikin fushi ko cikin kishi. Mafi muni da cutuwa shine a cikin soyayya a ce ɗaya na yaudarar guda. So wani darsashi ne a zuciya, wanda ke haddasa bege da ƙauna da sha’awa. Ya kan hana nutsuwa ko sukuni. Makanta ba iya rashin gani ce kawai da ƙwayar idanu ba, wanda yake ɗauke da zazzafar soyayya shi ma yana ɗauke da wannan makantar ta zuciya.
Mece ce makauniyar soyayya?
Makauniyar soyayya ita ce, irin soyayyar nan ta a mutu ko a yi rai, wacce ba a ji ba a gani yayin yin ta. Ita ce soyayyar da ba a hango gaba ko baya idan ana yin ta, Makauniyar soyayya illa ce ga mai yin ta, illar da ba a ganewa sai lokaci ya ƙure.
Yadda ake gane makauniyar soyayya:
Duk wanda ke cikin mayen soyayayya bai iya fahimta ya faɗa makauniyar soyayya sai dai wani ya ankarar da shi ko kuma sai bayan ya dawo hayyacinsa ta silar da-na-sani. Komai idan ya yi yawa ya ɓaci, idan har ba tsoron Allah ne ba. Don haka akwai wani mataki da ake kai wa soyayya take yin yawa.
Amma duk lokacin da ma’abota soyayya suka tsinci kansu a ɗaya ko kusan duka ko ma dukkan waɗannan, to la-shakka sun faɗa makauniyar soyayya, sai ko neman mafita da kyakkyawan fatan cimma ƙudiri na ƙwarai, yayin da ido ya rufe har aka kasa ganin laifin ɗaya aka kasa gane gaskiya da ƙarya ko da kuwa zai cutar da mai soyayyar akan kansa.
Yadda za a magance makauniyar soyayya:
Abin da zai zo zukatan mutane shine, yaya ɗan’adam zai magance abin da ba shi da iko da shi? Abin da lokacin da zai shiga zuciya ba ya shawara? Katsahan soyayya kan yi mamaya, ta ya ya za ka sami kwanjin tantance ta? To, amma Bahaushe ya ce, ‘idan hankali ya ɓata, hankali ke samo shi, kuma rigakafi ya fi magani’. Ga wasu matakai don rage kaifin makauniyar soyayya.
Addua
Addu’a babban makami ce ta hana faɗawa kan dukkan mummunar ƙaddara. Bakinmu ya saba da faɗin neman zaɓi na alkhairi wajen Ubangiji. Duk lokacin da aka haɗu da abin so a matsa da neman alkhairi a cikin haɗuwar.
Tsoron Allah
Son gaskiya shine, son da ake sa Allah cikinsa. Duk lokacin da shaiɗan ya yi galaba, ido ya rufe akan so, to fa an sami matsala.
Tarbiyyar iyaye:
Tarbiyyar iyaye da nuna wa yara illar da ke tattare da danƙa wa zuciya yarda da amana da sakin jiki da ‘ya’ya da hira da su da sa ido kan shige-da-ficensu na da tasiri ƙwarai kan dakushe kaifin afkawarsu kan makauniyar soyayya.
Son gaskiya:
Masoya ya kamata su fahimci soyayyar gaskiya. Masoyin gaskiya shine, kullum ke neman ɗaya ya zama abin alfahari ya zama nagari. Masoya su zama suna auna junansu a sikeli ta kaifin tunani su ware kalaman gaskiya da ke fitowa daga can ƙarƙashin zuciya da kalaman da iyakarsu baki. Da dama masoya sun faɗa tarko a dalilin kalamai na yaudara.
Bin iyaye:
Bijirewa iyaye ba hanya ce ta nuna soyayya ba. Masoyin ƙwarai shine wanda zai taimaka wa masoyinsa wajen biyayyar iyaye da neman albarkarsu.
Bincike:
Duk soyayyar da za a ƙulla ta babu bincike, to akwai matsala. A dalilin bincike za a gano illar da za a yi wa soyayyar birki tun kafin shaƙuwa. Sau da dama za a yi soyayya ta gani a faɗa, amma da an yi aure ba inda abin ke zuwa sai a rabu sakamakon rashin bincike a lokacin neman auren. Shi kuwa aure zaman gaskiya ne; makauniyar soyayya ba ta tasiri. Ko ta yi tasirin ɓoye halin da ba a so idan zama ya yi zama, dole sai an fahimta.
