2027: Gwamnoni masu ci da tsofaffi da ke takarar sanata

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Aƙalla tsoffin gwamnoni 18 na Nijeriya ne suke neman kujeru a Majalisar Dattawa gabanin babban zaɓen ƙasa na 2027, yayin da wasu gwamnonin da ke kan mulki su ma ke shirin barin gidajen gwamnati da nufin zuwa Majalisar Dokoki a matsayin sanatoci.

Wannan lamari na nuna yadda wasu ’yan siyasa da suka taɓa riƙe muƙamin gwamna, ciki har da waɗanda a halin yanzu suke sanatoci, ke ƙoƙarin sake komawa ko kuma ci gaba da kasancewa a majalisar dattawa bayan kammala wa’adinsu na mulki a jihohinsu.

Ga jerin sunayen ’yan siyasar da ke neman kujerun Majalisar Dattawa a zaɓen 2027:

1. Ibrahim Shekarau:

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya jagoranci jihar daga shekarar 2003 zuwa 2011. Ya kuma taɓa wakiltar mazaɓar sanatan tsakiyar Kano daga shekarar 2019 zuwa 2023. A zaɓen shekarar 2027, Shekarau na neman sake komawa majalisar dattawa bayan ya samu tikitin takarar jam’iyyar APC domin wakiltar mazaɓar sanatan tsakiyar Kano.

2. Inuwa Yahaya:

Inuwa Yahaya ya kasance gwamnan Jihar Gombe tun shekarar 2019, kuma ana sa ran zai kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2027. Yana cikin gwamnonin da ke shirin barin muƙamansu domin neman kujerun majalisar dattawa a zaɓen shekarar 2027.

3. Adamu Aliero:

Adamu Aliero ya kasance gwamnan Jihar Kebbi daga shekarar 1999 zuwa 2007. Tun bayan kammala mulkinsa, ya riƙa wakiltar mazaɓar sanatan tsakiyar Kebbi a majalisar dattawa a lokuta daban-daban. A yanzu haka yana neman sake samun kujerar a zaɓen da ke tafe.

4. Aminu Tambuwal:

Aminu Tambuwal ya kasance gwamnan Jihar Sakkwato daga shekarar 2015 zuwa 2023. Kafin zama gwamna, ya riƙe muƙamin shugaban majalisar wakilai ta ƙasa. A yanzu haka yana neman kujerar sanata a zaɓen shekarar 2027.

5. Mai Mala Buni:

Mai Mala Buni ya kasance gwamnan Jihar Yobe tun shekarar 2019. Yayin da wa’adinsa na biyu ke daf da ƙarewa, yana neman sauya sheƙa daga gidan gwamnati da ke Damaturu zuwa majalisar tarayya domin zama sanata.

6. Yahaya Bello:

Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, na neman kujerar sanata domin wakiltar mazaɓar sanatan tsakiyar Kogi. Bello ya jagoranci Jihar Kogi daga shekarar 2016 zuwa 2024, kafin ya kammala wa’adinsa na mulki. Yana takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC, inda zai fafata da sauran ’yan takara, ciki har da sanatar da ke kan kujerar a yanzu, Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

7. AbdulRahman AbdulRazaƙ:

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, na neman kujerar sanata a zaɓen shekarar 2027, inda zai fafata domin wakiltar mazaɓar sanatan tsakiyar Kwara a ƙarƙashin jam’iyyar APC. AbdulRazaƙ, wanda ya hau kan karagar mulki a shekarar 2019, ana sa ran zai kammala wa’adinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayun 2027. Bayan haka kuma yake shirin komawa majalisar tarayya.

8. Dapo Abiodun:

Dapo Abiodun ya zama gwamnan Jihar Ogun a shekarar 2019, sannan ya sake lashe zaɓe a shekarar 2023 domin samun wa’adi na biyu na shekaru huɗu. Yana neman kujerar sanata ne bayan kammala wa’adinsa na biyu a matsayin gwamna.

9. Simon Lalong:

Simon Lalong ya kasance gwamnan Jihar Filato daga shekarar 2015 zuwa 2023. Ya samu tikitin takarar sanata na jam’iyyar APC domin wakiltar mazaɓar Kudancin Filato a zaɓen fidda gwani na ’yan takarar majalisar tarayya da jam’iyyar ta gudanar a watan Mayun 2026.

10. Mukhtar Ramalan Yero:

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya jagoranci jihar daga shekarar 2012 zuwa 2015. A zaɓen 2027, yana neman kujerar sanata domin wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa a ƙarƙashin jam’iyyar APC. Zai fafata da sauran ’yan takara, ciki har da sanatan da ke kan kujerar a yanzu, Khalid Ibrahim Mustapha, na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

11. Ahmadu Fintiri:

Ahmadu Fintiri ya kammala wa’adinsa biyu na mulkin Jihar Adamawa, inda ya kasance gwamna daga shekarar 2019 zuwa 2027. A yanzu yana neman kujerar sanata mai wakiltar mazaɓar tsakiyar Jihar Adamawa. Wannan ne karon farko da yake neman zama sanata.

12. Bala Mohammed:

Shi ma Bala Mohammed ya kammala wa’adinsa biyu na mulkin Jihar Bauchi, inda ya kasance gwamna daga shekarar 2019 zuwa 2027. Kafin zama gwamna, ya taɓa riƙe muƙamin minista, sannan ya kasance sanata mai wakiltar mazaɓar Kudancin Bauchi. A zaɓen 2027, yana neman sake komawa majalisar dattawa domin wakiltar jihar.

13. Godswill Akpabio:

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya na yanzu, kuma tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, na neman sake lashe zaɓen sanata a ƙarƙashin jam’iyyar APC. Akpabio ya jagoranci Jihar Akwa Ibom daga shekarar 2007 zuwa 2015. Tun daga shekarar 2019 yake wakiltar mazaɓar sanatan Arewa maso Yammacin Akwa Ibom a majalisar dattawa. A yanzu haka yana neman sake samun wa’adi a majalisar bayan ya samu tikitin takarar jam’iyyar APC domin wakiltar wannan mazaɓa.

14. Orji Kalu:

Orji Kalu ya yi gwamnan Jihar Abia daga shekarar 1999 zuwa 2007, kafin ya koma harkokin siyasar majalisa a shekarar 2019. Ya samu tikitin takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027, inda yake neman sake komawa majalisar dattawa domin ci gaba da wakiltar mazaɓar sanatan Arewa ta Jihar Abia.

15. Adams Oshiomhole:

Adams Oshiomhole ya kasance gwamnan Jihar Edo daga shekarar 2008 zuwa 2016. A shekarar 2023 kuma aka zaɓe shi a matsayin sanata mai wakiltar mazaɓar Arewa ta Jihar Edo a ƙarƙashin jam’iyyar APC. A yanzu yana neman sake samun wani wa’adi a majalisar dattawa.

16. Henry Seriake Dickson:

Tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Henry Seriake Dickson, ya jagoranci jihar daga shekarar 2012 zuwa 2020. Yana neman sake lashe zaɓen sanata domin ci gaba da wakiltar mazaɓar Yammacin Bayelsa a majalisar dattawa. Ba kamar sauran tsoffin gwamnoni da dama da ke cikin wannan jerin ba, Dickson yana takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).

17. Ifeanyi Okowa:

Tsohon gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya jagoranci jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023. Kafin zama gwamna kuma, ya wakilci mazaɓar Arewacin Delta a majalisar dattawa daga shekarar 2011 zuwa 2015. A zaɓen 2023, Okowa ya kasance ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP. Sai dai daga baya ya samu tikitin takarar jam’iyyar APC domin neman kujerar sanata a zaɓen 2027.

18. Hope Uzodimma:

Gwamnan Jihar Imo na yanzu, Hope Uzodimma, ya shafe shekaru yana jagorantar jihar tun bayan hukuncin kotu da ya tabbatar da nasararsa a zaɓen gwamna na shekarar 2020. Yana neman komawa majalisar dattawa, inda a baya ya taɓa wakiltar shiyyar Orlu ta Jihar Imo.

Yawaitar tsoffin gwamnoni da suke neman kujerun sanata ya sake jawo hankalin jama’a kan yadda ’yan siyasar da suka taɓa riƙe muƙaman zartarwa ke ƙoƙarin komawa ɓangaren majalisa. Haka kuma, wannan al’amari ya haifar da tambayoyi kan irin tasirin da tsoffin gwamnoni ke da shi a jihohinsu, musamman ganin cewa wasu daga cikinsu za su fafata ne da sanatocin da ke kan kujeru da kuma wasu manyan ’yan siyasa. Komawarsu majalisar tarayya na iya yin tasiri ga tsarin wakilci da kuma yadda za a raba muƙaman shugabanci a majalisar dattawa ta 11, gwargwadon sakamakon zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi

Leave a Reply