Daga SANI GAZAS CHINADE Damaturu
Shahararren malamin addinin musuluncin nan da ke garin Maiduguri cikin jihar Borno Sheikh Sheriff Saleh wanda ya yi hijira ya bar garin na Maiduguri yayin da garin ke tsaka da fituntunin ‘yan bindigar Boko Haram a shekarun baya, ya koma gida sakamakon samun zaman lafiya da aka yi.
Masoyan malamin addinin Musuluncin Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh El-Hussaini sun taru a filin jirgin sama na Muhammadu Buhari, Maiduguri, a ranar Lahadi domin maraba da shi a lokacin da ya dawo jihar Borno bayan shekaru 15 da barin babban birnin jihar.
Mataimakin Gwamna Umar Usman Kadafur, wanda ya wakilci Gwamna Babagana Umara Zulum, ne ya jagoranci tawagar gwamnati da ta tarbi malamin a ranar Lahadi, 15 ga Nuwamba, 2026.
Tawagar ta haɗa da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Jere, Ahmed Satomi, da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa, da mambobin majalisar zartarwa ta jihar, da shugabannin addini, da kuma malaman addinin musulunci.
Ɗimbin jama’a masu fatan alheri suma sun taru a filin jirgin, lamarin da ya sanya zuwan nasa ya zama wani muhimmin abu ga magoya bayan malamin.
Mabiya da dama suna ɗaukar Sheikh Sheriff a matsayin malamin addini, mai ba da shawara, da kuma jagora wajen karantarwa da wa’azin addinin musulunci tare da amsa fatawa.
Dawowarsa ta samar da sabon babi ga harkokin addini lura da cewar ya daɗe baya cikin garin na Maiduguri.
Da yake magana a madadin gwamna da gwamnatin jihar, mataimakin gwamnan Umar Usman Kadafur ya yi maraba da malamin tare da gode wa Allah bisa dawowarsa lafiya.
Ya yi addu’ar samun zaman lafiya da gamsarwar zama a Maiduguri, yayin da yake bayyana fatan samun kyakkyawar fahimtar juna ta addini, haɗin kai, da kuma zaman lafiya a faɗin Borno.
Wannan komawa gida na zuwa ne a yayin da al’ummomi a faɗin Borno ke ci gaba da fuskantar sakamakon rikicin tashin hankali na tsawon shekarun da ya haifar.
Shugabannin addini na ci gaba da zama muhimman mutane wajen cuɗanya da al’umma, musamman wajen inganta zaman lafiya, sake gina alaƙar zamantakewa, da kuma ƙarfafa tattaunawa.
