Peter Obi ta yi tir da farmakar ayarin motocin Kwankwaso, ya nemi a kamo masu hannu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Lahadi, 15 ga Nuwamba, 2026 wasu da ake zargin ‘yan daba ne, suka ƙaddamar da farmaki akan ayarin motocin tsohon Gwamnan Jihar Kano Kano kuma abokin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi a zaɓen 2027, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, a lokacin da suka kai ziyarar yaƙin neman zaɓe a Ƙaramar Hukumar Bichi da ke jihar.

Kakakin ɗan takarar gwamnan, Kwamared Ibrahim Garba Shu’aibu ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga ‘yan jarida, inda ya ce maharan sun raunata wasu mambobin tawagar yaƙin neman zaɓen da lalata motocinsu.

A cewarsa, da fari tawagar ta kai ziyara ne zuwa ƙananan hukumomin Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Ɓagwai cikin nasara ba tare sa fuskantar wani hargitsi ba. Daga bisani an sanar da tawagar cewa wasu mutane da ke adawa da yaƙin neman zaɓen sun tare hanyar zuwa yankin Bichi.

Obi, a wata wallafa ta kafar X a yau Litinin, ya yi alla-wadai da harin, inda ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan uwansa kuma abokin tafiya, sannan ya bayyana alhininsa kan al’amarin. “Ina matuƙar baƙin ciki kan rahotannin hari akan ayarin motocin ɗan uwana kuma abokin tafiya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da mambobin tawagarsa a Ƙaramar Hukumar Bichi ta Jihar Kano,” inji shi.

Tsohon Gwamnan Anambran ya ce bai dace a riƙa amfani da bambance-bambancen siyasa wajen tayar da tarzoma ba, wulaƙantawa ko lalata dukiyoyi ba.

Akan haka ne ya yi kira ga rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su ɗauki matakin bincike kan al’amarin da gurfanar da waɗanda aka samu da hannu a ciki har da waɗanda suka ɗauki nauyi don tabbatar da adalci

By Babaji

Leave a Reply