Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da kayan tallafi ga matasa da mata

Spread the love

Daga SANI GAZAS CHINADE Damaturu

Gwamnatin Jihar Yobe ta ƙaddamar da rarraba kayan tallafi ga matasa da mata 500, waɗanda suka haɗa da babura masu taya uku nau’in akori kura (Jega), baburan hawa masu taya biyu, kekunan dinki, ga waɗanda suka ci gajiyar shirin a faɗin gundumar mazabar ɗan majalisar dattawan Kudancin Jihar a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafawa matasa, dogaro da kai na tattalin arziki da kuma bunƙasa rayuwa.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar a Gadaka, ƙaramar hukumar Fika, Gwamna Mai Mala Buni, wanda ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC Alhaji Baba Mallam Wali ya wakilta.

Da yake jawabi a wurin taron, Baba Malam Wali ya bayyana cewa shirin yana nuni ne da ƙudurorin gwamnati na samar da damar tattalin arziki ga al’umma, musamman matasa, ta hanyar ba su kayan aikin da za su zama masu dogaro da kai da kuma kasancewa mambobi masu amfani a cikin al’umma.

Ya bayyana cewa rarraba kayan tallafin an tsara shi ne domin taimaka wa waɗanda suka ci gajiyar shirin wajen kafa hanyoyin rayuwa masu ɗorewa, inganta matsayinsu na tattalin arziki da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban al’ummominsu.

Wali ya ƙara da bayar da tabbacin cewa, idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta ci gaba da ayyukan raya ƙasa na Gwamna Buni, musamman waɗanda suka mayar da hankali kan ci gaban matasa, ƙarfafawa tattalin arziki da inganta rayuwa.

Ya jaddada cewa ci gaba zai kasance ginshiƙin tafiyar gwamnatinsa, tare da ƙara ba da mayar da hankali ga shirye-shiryen da ke samar da dama ga matasa da kuma ba su damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban tattalin arzikin jihar.

Ɗan takarar na jam’iyyar APC ya yi amfani da damar wajen yin kira ga al’umma da su kaɗa ƙuri’a da yawa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar, inda ya ba da misalai da ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen da aka ƙaddamar a jihar da kuma ƙasar baki ɗaya.

Rarraba kayan tallafin guda 500 wanda ya haɗa da baburan hawa guda 200, babura masu taya uku (Jega) 100 da kekunan dinki 100 ga wadanda suka ci gajiyar shirin waɗanda suka hada da matasa, mata da sauransu an yi shi ne domin inganta tattalin arzikin su da kuma magance rashin aikin yi ta hanyar matakan tallafi na zahiri.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin Malam Muhammad Umar ya bayyana godiyar sa ga gwamnatin jihar Yobe dangane da yadda ta basu wannan tallafi, kana ya bada tabbacin za su yi amfani da wannan babur mai taya uku wajen neman abin kan sa.

By ukarofi

Leave a Reply