Sojoji sun daƙile hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara, sun ƙwato makamai a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro ƙarƙashin Atisayen FANSAR YAMMA, sun yi nasarar daƙile wasu hare-haren ‘yan ta’adda a jere a ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Anka da ke Jihar Zamfara, sannan sun halaka wani ɗan ta’adda a Jihar Kaduna. An gudanar da atisayen ne a ranar 14 ga Nuwamba, 2026, waɗanda suka yi sanadiyyar ƙwato makamai, babura, wayar hannu da wasu ababe da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce sojojin Sashe na Biyu sun daƙile hare-hare da wasu ‘yan bindiga akan babura suka yi yunƙurin ƙaddamarwa a ƙauyukan Wuya da Yarzabiya da ke Anka. Kasancewar ƙarfin makaman sojojin ya fi nasu, hakan ya sa suka kora ‘yan ta’addar tare da tilasta musu janyewa daga kai farmakin. Amma, ‘yan bindigar sun sake shiryawa tare da yunƙura a karo na biyu, inda dakarun suka sake daƙilewa cikin salon ƙwarewar aiki.

Daga bisani an tura ƙarin wasu jami’ai daga wasu ƙauyuka, yayin da sojoji suka cigaba da sintiri a yankunan don kauce wa fuskantar wani hari. Sanarwar ta ce ‘yan ta’addar sun yi ƙoƙarin sace wasu dabbobi ne daga ƙauyukan amma ba su yi nasara ba sakamakon harin sojin sama da ya halaka da dama daga cikinsu.

A wani atisayen dakarun a Kaduna, jami’an Sashe na Ɗaya sun gudanar da sintirin faɗa a yankunan wasu gonaki da ke ƙauyen Kajuru, biyo bayan wasu rahotannin sirri kan ayyukan ‘yan ta’adda. Bayan musayar wuta a tsakanin ɓangarorin biyu, an yi nasarar halaka ɗaya daga cikin ‘yan ta’addar yayin da sauran suka tsere. Yayin bincike, an gano wasu bindigu guda biyu, wayar hannu, tabar wiwi, da wasu miyagun ƙwayoyi da kuma katinan kira.

Haka ma a yankin hanyar Buruku zuwa Kaduna, inda aka yi arangama tsakanin ‘yan ta’adda da dakarun tsaro bayan samun bayanan sirri, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa da barin babura guda biyu da jami’an suka ƙwato.

A ƙarshe, rundunar ta yi kira ga al’umma da su riƙa bai wa sojoji bayanan dukkan wani abin zargi a yankunansu don taimakawa ayyukan daƙile miyagun laifuka da dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a Arewa maso Yamma da ma sauran sassan Nijeriya baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply