
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan Sanda a Birnin Tarayya Abuja, ta ce za a sako mutane guda 78 ɗin nan da aka ce an kama su bisa zargin kai wa ayarin motocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu hari daga komar hukuma, bayan da shugaban da kansa ya amince da yafe musu.
A sanarwar da Kakakin rundunar, Josephine Adeh ta fitar a yau Litinin, an ce an kama mutanen ne bayan harin da aka kai wa ayarin motocin a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, a Masallacin Shehu Shagari da ke Gundumar Garki a Abuja.
Al’amarin ya auku ne jim-kaɗan bayan kammala sallar Juma’a, “inda ‘wasu mutane suka riƙa jifa da duwatsu da wasu ababe masu haɗari, wanda ya haifar da dameji ga motoci da dama da raunata wasu jami’an tsaro,” inji sanarwar.
A yayin haka ne wata haɗakar jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin ‘yan sanda ta gaggauta ɗaukar mataki tare da gudanar da binciken leƙen asiri, inda ta yi nasarar kama mutane da dama da aka danganta su da hannu a laifin, waɗanda adadinsu ya kai 78.
Ta ƙara da cewa, bayan yafiyar, fadar shugaban ƙasar ta kuma umarci a gargaɗi waɗanda ake zargin tare da sakin su.
Kazalika, ta ce Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Ahmed Sanusi ya ja kunnen al’umma akan ƙaurace wa ayyukan da za su tayar da tarzoma gabanin zaɓukan 2027, yana mai cewa za a hukunta dukkan wanda aka samu hannu a saɓa wa doka ba tare da la’akari da kowaye ne ba. Sanarwar ‘yan sanda ita ce jawabin farko a hukumance kan harin.
