
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Harkokin karatu a manyan makarantun gwamnati a Jihar Kaduna sun samu tsaiko daga sababbin al’amuran rikicin ƙwadago, inda Ƙungiyar Malaman Makarantun Polytechnics (ASUP) ta fara yajin aiki kan rashin bayan mambobinsu alawus.
Haka kuma, Kwamitin Haɗaka na Ɗaukar Mataki (JAC) na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ya dakatar da yajin aikin gargaɗi na mako guda bayan tattaunawarsu da gwamnatin jihar. Waɗannan ci-gaba sun zo ne a ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026 yayin da gwamnatin jihar da hukumomin gudanarwar makarantun suke ƙoƙarin magance koken da ƙungiyoyin ƙwadago suka gabatar.
Yajin aikin na ASUP ya biyo bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 15 da ta bai wa gwamnatin Kaduna kan rashin aiwatar da alawus ɗin mambobinta na CATA da EAA, waɗanda ke ƙarƙashin yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar.
A cewarta, ta ɗauki matakin ne domin warware matsalolin da aka gabatar wa gwamnatin waɗanda ke ƙarƙashin yarjejeniyar FGN-ASUP na 2026 domin ta hanzarta aiwatarwa ganin cewa an ɗauki tsawon lokaci ana jiran haka.
Da yake zantawa da wakilin Blueprint, Shugaban ASUP na Kaduna na reshen makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic (NBPZ) kuma Shugaban kwamitin JAC kuma Shugaban JUTIKS, Kwamared Usman Shehu Sulaiman, ya bayyana cewa rikicin CATA da EAA na da bambanci da na gama-gari da jagorancin ASUP ya umarta kan kaso 40 na gyaran tsarin albashi na CONRAISS.
