
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NDC, Barista Ibrahim Kashim ya fice daga jam’iyyar tare da koma wa mai mulki (APC), lamarin da ya kawo ƙarshen zamansa a ɓangaren adawar gabanin zaɓukan 2027.
Kashim, wanda tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi (SSG) ne, ya sanar da ficewarsa ne a ranar 16 ga Nuwamba, 2026 a Sakatariyar APC da ke Bauchi, inda ya samu tarba daga mambobi da magoya bayan jam’iyyar. Matakin nasa ya zo ne kusan wata guda bayan ajiye matsayinsa na mamba a NDC a ranar 16 ga Oktoba, 2026, yana mai cewa ya yi hakan ne saboda wasu dalilansa da kuma shawarwari da makusantansa.
Wannan ci-gaba na da muhimmanci musamman duba da cewa sunansa ya fito a jaddawalin ‘yan takarar gwamna da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta riga ta fitar don zaɓen 2027. A cewarsa, ya koma APC ne saboda jam’iyyar ta samar wa jihar Bauchi fagen siyasa mai ƙarfi domin janyo muhimman ayyukan ababen more rayuwa, zuba jari da damarmakin ci-gaba daga Gwamnatin Tarayya.
Tsohon Sakataren ya kuma kirayi magoya bayansa, abokan siyasa da masu ruwa da tsaki da su koma APC, yana mai cewa matakin nasa na da nufin ciyar da jihar gaba da inganta rayukan al’umma musamman mata da matasa ta samar musu da ayyuka dogaro da kai.
Wannan al’amari dai ya jefa NDC a halin rashin tabbas, inda shugabanta na jihar Abdullahi Misau ya ce jagorancinsu bai ji daɗin matakin ba, don haka za su nemi shawarwarin shari’a kan tasirin al’amarin. Ya ƙara da cewa, jam’iyyar za ta cigaba da fafutukar neman zaɓe gabanin 2027.
