Tinubu na shirin fitar da talakawa miliyan 80 daga talauci ta shirin $500m NG-CARES

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya na harin fitar da ‘yan Nijeriya tsakanin miliyan 50 da miliyan 80 daga cikin ƙangin talauci ta hanyar faɗaɗa shirin tallafin COVID-19 (NG-CARES), biyo bayan nasarar da aka samu a zangon farko da ya fitar da mutane miliyan 17 daga talauci a Nijeriya.

Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattali ta Tarayya ce ta bayar da ba’asin wannan ci-gaba a ranar Litinin a Abuja, a wani zaman ‘yan kwamitin shirin don bunƙasa shi ta fuskar kuɗi.

Ministan ma’aikatar, Sanata Abubakar Bagudu, ya ce an shirya NG-CARES ne da nufin kare talakawan Nijeriya daga fuskantar ƙalubalen tattali da tasirin gyare-gyaren tattalin arziƙi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu take yi don ciyar da al’umma da ƙasar gaba.

Ya bayyana cewa, duk da cewa gyare-gyaren tattali suna da muhimmanci wajen daidaita al’amuran Nijeriya, tasirinsu yana shafar magidanta da yankuna da dama, wanda ya sa gwamnatin ta ga cewa wajibi ne ta ɗauki matakin rage raɗaɗinsa.

Ya ce, ababen da aka fahimta daga annobar COVID-19 sun nuna cewa wasu al’amura da ba a yi zaton aukuwarsu ba ka iya rage wa gwamnati adadin kuɗaɗen shiga da kassara ƙarfin tattali ga ɗaiɗaikun mutane da yankuna daga iya jure wa matsin tattali.

Ya kuma ƙalubalanci jihohi da su yi amfani da Dala miliyan 500 da ake da shi a matsayin dama wajen aiwatar da shirye-shiryen zamantakewa da tattali da ka iya janyo zuba jari, yana mai kira ga jami’an shirin da su jagorancin aikin aiwatarwa bisa inganci.

By Babaji

Leave a Reply