
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun halaka wani ɗan Chana mai shekara 37 da ke aikin haƙar ma’adinai, Wang Tingjian, wanda kuma ke aiki da kamfanin Zurfi Mining Company tare da ɗan sandan da ke masa rakiya, Abba Ya’u mai aiki a ofishin ‘yan sandan mobile na MOPOL 34 a Jihar Gombe, a lokacin da suka yi musu kwanton-ɓauna. Al’amarin ya auku ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 1:30 na rana a ƙauyen Rugar Gundumar Gwana ta Ƙaramar Hukumar Alkalerin jihar.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga ‘yan jarida a ranar Litinin, Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Nafi’u Habib, ya ce an farmaki ɗan Chanan ne a lokacin da yake gudanar da bincike kan wani wajen haƙar ma’adinai tare da ɗan rakiyar nasa.
Ya bayyana cewa, an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan yayin aukuwar lamarin, wanda ya haifar da sun jikkata sakamakon harbin bindiga. Cikin hanzarta aka garzya da su zuwa Babban Asibitin Koyarwa na Gombe. A nan ne aka tabbatar da mutuwarsu, sannan aka ajiye gawarwakinsu a ɗakin ajiyar gawa.
Ya ƙara da cewa, jami’ansu na sashen yaƙi da garkuwa da aikata miyagun laifuka tare da haɗin-gwiwar sojoji da ‘yan bijilante sun fara gudanar da aikin farauto maharan. Kazalika, ya ce hukumomin tsaro suna aiki wajen gano ainihin yadda al’amarin ya auku.
