Kyautar kuɗaɗe ga talakawa abin a yaba ne

Spread the love

Ina amfani da wannan dama wajen yaba wa tsarin rabon kuɗaɗe ga jama’a, domin ga dukkan alamu, ba a nuna wariya ko fifita wani ɓangare a kan wani ba wajen gudanar da wannan rabon.

Duk da cewa ana cewa ba a gaggawar yabon ɗan kuturu sai ya girma kuma ya mutu da yatsunsa, amma ina ganin ya dace a yaba wa abin da aka yi na alheri idan an ga alamun adalci a cikinsa.

Ya kamata jama’a mu nutsu. Duk wanda ya samu rabonsa, ya gode wa Allah, wanda kuma bai samu ba, ya guji hassada da ƙyashi ga waɗanda suka dace da rabon.

A gefe guda kuma, ina fatan kada wasu masu mugun nufi su yi amfani da wannan dama wajen yaudarar jama’a, musamman ganin yadda mutane da dama ke ɗokin jin saƙon rabonsu.

Saboda haka, ya kamata kowa ya yi taka-tsantsan, domin wannan batu na rabon kuɗaɗe yana buƙatar kulawa ta musamman. Kada wasu mutane marasa kyakkyawar manufa su yi amfani da halin da ake ciki wajen damfarar jama’a ko aika musu da saƙonnin yaudara, musamman ganin yadda mutane da dama ke jiran samun labarin rabonsu.

A ƙarshe, ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya nesantar da mu daga talauci, Ya kuma ba shugabanninmu ikon gudanar da mulki cikin adalci da gaskiya.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa a Katsina 07066434519/08080140820.

By ukarofi

Leave a Reply