
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunayen wasu mutane biyu ga majalisar dokoki ta jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni da mambobin majalisar manyan jami’an gwamnatin jihar.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana haka cikin wata takarda a jiya Asabar.
Waɗanda aka bada sunayen nasu sune Barista Abdulkarim Kabir Maude daga Ƙaramar Hukumar Minjibir da Dakta Aliyu Isa Aliyu, wanda Farfesa mai daraja ta biyu ne shi a tsangayar Lissafi Mai faɗi.
Barista Maude, wanda ɗan shekara 40 ne a yau ne yake shirin zama babban lauya wato SAN, inda za a tabbatar da shi a Kotun Ƙoli.
Haka kuma, babban lauyan ya kammala karatunsa na digirin farko a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a fannin shari’a.
Sannan, mamba ne shi a ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa, wato ‘Nigerian Bar Association’ da Cibiyar ‘Chartered Institute of Arbitrators of Nigeria’, inda ya samu gogewa a ɓangarori da dama na shari’a da kuma riƙe wasu muƙamai a ofisoshi daban-daban.
Shi kuwa Dakta Aliyu Isa mai shekaru 41, ya yi digirinsa na farko ne a tsangayar Lissafi ta Jami’ar Bayero da ke Kano, sai na biyu a irin tsangayar daga Jami’ar Jordan ta Kimiyya da Fasaha da kuma na uku a Jami’ar Firat da ke Turkiyya.
