
Gwamnatin Tarayya ta kirayi ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da gas (PENGASSAN) da Matatar Dangote da su jingine rikicin da ke tsakaninsu.
Hakan ya biyo bayan gayyata ta musammam da ta yi wa ɓangarorin biyu domin shiga tsakani.
A yau Lahadi PENSASSAN ta sanar da fara yajin aiki a ƙasa baki ɗaya sakamakon abinda ta kira da korar ma’aikata da matatar Ɗangote ta yi bayan sun ayyana muradinsu na shiga ƙungiyar.
Ministan Ƙwadago, Maigari Dingyaɗi ya bayyana cewa wakilan ɓangarorin biyu za su gana da juna a hedikwatar ma’aikatarsa da ke Abuja.
“Ina neman ɓangarorin biyu da su tunan muhimmancin ɓangaren fetur da gas ga Nijeriya, saboda shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin ƙasa”, inji Ministan, a wata sanarwa daga ofishinsa yau Lahadi.
“Yajin aiki ba asarar kuɗin shiga kawai zai jawo ga ƙasa ba, zai ƙaro wahalhalu ga ƴan Nijeriya. Daga baya ma zai yi tasiri a ɓangaren tsaron ƙasa,” inji sanarwar da Patience Onuobia.
