Shettima ya zarce Jamus bayan Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Spread the love

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bar birnin New York a yau Lahadi, bayan kammala wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80, wato UNGA 80.

Shettima ya halarci taron ne a madadin shugaban kasa, inda ya jagoranci wakilan Nijeriya a zaman tattaunawa da manyan shugabannin duniya, cibiyoyi na ƙasa-da-ƙasa da kuma ƴan kasuwa masu zuba jari.

Bayan kammala taron, Shettima ya bar Amurka zuwa Jamus, domin cigaba da wasu muhimman ayyuka da s0uka shafi tattalin arziƙi da kuma bunƙasa haɗin-gwiwar Nijeriya da ƙasashen duniya.

A yayin zaman nasa a New York, Shettima ya halarci taruka da dama, ya gabatar da jawabi a madadin Najeriya, tare da ƙarfafa ƙudirin gwamnatin Tinubu na kawo cigaba ta hanyar haɗin-gwiwar ƙasa-da-ƙasa musamman wajen yaƙi da sauyin yanayi, bunƙasa tattalin arziƙi da kuma zaman lafiya a Nahiyar Afirka.

By Babaji