Gwamnan Neja ya soke gangamin APC, ya ayyana makokin kwana uku kan mutuwar masu haƙar ma’adanai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da soke taron gangamin siyasar jam’iyyarta ta APC wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar a Minna, bayan mutuwar mutane 37 a ofishin Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) reshen Jihar Neja.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa labaran Jihar, Bologi Ibrahim ya fitar a ranar Juma’a, Gwamna Umaru Bago ya bayyana kaɗuwarsa kan al’amarin gami da miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda iftila’in ya shafa.

Gwamnan ya kuma ayyana makokin kwana uku domin jimamin mutuwar mutanen. Gwamnatin ta ce wannan mataki ya biyo bayan faruwar abin alhinin ne domin karrama mamatan da kuma iyalansu.

Da fari dai an shirya gudanar da gangamin APCn ne a Minna a ƙarshen wannan mako. Haka kuma, gwamnatin ta umarci hukumomin tsaro da su ɗauki matakan da suka dace kan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply