Gwamnati ta cire darasin lissafi a sharaɗin shiga manyan makarantu ga ƴan kimiyyar zamantakewa

Spread the love

A yanzu daliban da ke ɓangaren kimiyyar zamantakewa, wato Social Science ko Arts a sakandare suna na damar samun gurbin shiga jami’a ko da ba su ci darasin lissafi ba wato Mathematics.

Gwamnatin tarayya ce, ta sanar da cewa daga yanzu darasin lissafi wato Mathematics ba dole bane ga daliban bangaren Art wajen niman gurbin shiga Jami’a.

A wata sanarwa da ministan Ilimi ya fitar ta hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo yace an dauki matakin ne a cikin sauye-sauyen da ake yi a bangaren Ilimi.

A karkashin Sabon tsarin, a yanzu darasin lissafi (Mathematics) zai zama zabi ne ga duk dalibin dake bangaren Arts da wasu kwasa- kwasai Koda yake ga daliban dake bangaren Kimiyya da safaha wato Science, Technology, and Social Science ya zama musu dole har yanzu sai Suna da darasin lissafi.

Sanarwar ta kara da cewa anyi sauye-sauyen ne don baiwa dalibai daman Samun gurbin shiga manyan makarantu tare da cire wasu takunkumi da ke hana dalibai Samun damar shiga manyan makarantu don niman Ilimi.

Sanarwar ta Kuma yi kira ga manyan makarantu su tabbatar an aiwatar da Wannan tsarin yadda ya kamata don ci gaban Ilimi a kasarnan.

By Babaji