Daga USMAN KAROFI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana ƙoƙarin tabbatar da bunƙasar noma da wadatar abinci a Najeriya ta hanyar haɗin gwiwa da cibiyoyin bincike da samar da amfanin gona, musamman cibiyar nazarin noma ta IITA. Ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai cibiyar IITA da ke Ibadan, inda ya ce lokaci ya yi da za a ɗauki matakin zahiri wajen magance matsalar ƙarancin abinci a ƙasar.
A yayin taron, daraktan IITA, Dr. Simeon Ehui, ya bayyana cewa cibiyar na jagorantar shirye-shirye da suka haɗa da samar da iri masu jure sauyin yanayi, da fasahohin noma masu amfani. Ya ce aikin haɗin gwiwa tsakanin IITA da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa yana taimakawa wajen haɓaka amfanin gona kamar rogo, masara, wake da shinkafa. Har ila yau, ya bayyana cewa an kafa wata cibiya ta musamman a IITA don inganta amfani da takin zamani da kuma haɓaka lafiyar ƙasa domin bunƙasa noma a Najeriya.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da IITA domin amfani da sabbin fasahohi na noma da kuma bunƙasa harkar samar da abinci. Ya kuma yaba da ƙoƙarin IITA wajen taimakawa manoma a yankin Arewa maso Gabas, inda suke samar da ayyukan yi ga matasa da mata, tare da bunƙasa samar da abinci mai gina jiki.
Tawagar mataimakin shugaban ƙasa ta ziyarci wurare da dama a cibiyar, ciki har da cibiyar sarrafa iri na rogo da doya, da kuma dandalin kasuwanci na IITA. A yayin ziyarar, mataimakin shugaban ƙasa yana tare da ministan noma da wadatar abinci, Sanata Abubakar Kyari, da wasu manyan jami’an gwamnati, inda suka jaddada ƙudirin gwamnati na yin amfani da binciken noma domin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
