“Karatu na sanya mutum ya kasance mai nagarta da kyautata ɗabi’a”
Ba na damuwa da jigon labari fiye da yadda nake damuwa a kan taurarin labarin
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Malam Ado Bala, marubucin littafin, ‘Husufin Farinciki’, wanda ya yi nasarar zama na uku a Gasar Tsangayar Gusau na shekarar 2019, irin marubutan nan ne da ake ce wa taurarin ɓoye, waɗanda ba su cika bayyana kansu ko su kururuta basirar da Allah ya yi musu ba, sai ga wanda ya gano su ko ya kusance su. Alhalin kuwa, Malam Ado tauraro ne na nuna wa Sarki, saboda baiwar da Allah Ya yi masa ta ƙirƙirar labari, da isar da saƙo cikin hikima. Shi ne mai kantin sayar da littattafan nan na ‘Chapter One’ da ke birnin Kano, wanda ya shahara wajen sayar da littattafan adabi na Hausa da Turanci. A tattaunawar sa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Ado Bala ya bayyana abin da ya fi jan hankalinsa yayin rubutun labari, wanda marubuta da masu karatu za su yi mamakin jin cewa, ba jigon labari ba ne!
MANHAJA: Za mu fara da jin cikakken sunanka.
ADO BALA: Assalamu alaikum. Sunana Ado Abubakar Bala. Ni dai kamar yadda kowa ya san ni marubuci ne. Mutane sun daɗe suna yi min kallon marubuci tun ma kafin na fitar da littafina. Harwayau, ni mutum ne mai sha’awar zane-zane, wanda ake kira da ‘artist’ da Ingilishi.
Ko za ka gaya mana wani abu daga tarihin rayuwarka?
To, da farko dai ni haifaffen Jihar Kano ne daga ƙaramar Hukumar Dala. Na shiga firamare a ƙarshen shekarun tamanina (1980s), bayan na fara karatun Islamiyya. Na yi firamare a makarantar firamare ta Magwam a nan cikin Kano. Na kuma yi karatun sakandire a makarantar Gwamnatin Tarraya ta FGC Daura a Jihar Katsina. Na kammala a shekarar 2001, daga nan na shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 2004, na kammala a shekarar 2009. A yanzu haka ina aiki ne da Gwamnatin Tarayya a Hukumar Jarabawar Ilmin Larabci da Addinin Musulunci ta ƙasa (NBAIS). Kuma Allah Ya albarkace ni da aure da yara biyu, duk mata. Ina zaune a garin Kano.
Wanne matakin rayuwa ko ƙalubale ka tsallake har zuwa matakin da kake a yanzu?
Alhamdulillah. An tsallake matakai da yawa, kuma an yi nasara. Tun daga kan karatu zuwa gina kasuwanci da ajiye iyali waɗannan duk nasarori ne na rayuwa da za a gode wa Allah.
Ko za ka iya tuna abin da ya fara sa maka sha`awar karance-karance da rubuce-rubuce?
E to, na taso tun ina yaro na ga gidanmu da littattafan Hausa kamar su Tatsuniyoyi Da Wasanni, Ruwan Bagaja, Magana Jari Ce da sauransu. Tun ban ma iya karatu ba ina iya buɗe littafi na kalli hotuna, har zuwa lokaci da na fara karantawa da kaina. Lokacin da na yi nisa a karatun littattafan Hausa, bayan na kammala sakandire daga nan na ji sha’awar son rubutu ta fara shiga ta.
Wanne tasiri harkar karatu da adabi suka yi ta hanyar inganta rayuwarka?
Haƙiƙa tasirin da karatu ya yi a kaina yana da yawa, da farko dai ya sanya min tunanin tantance duk wani abu da na gani a rayuwa. Idan har ka yi karatu da yawa, to da wahala ka karɓi kowanne irin tunani kai tsaye, dole ne sai ka kalle shi ta fuskoki da yawa. Karatu na sanya mutum a karan kasa ya kasance mai nagarta da kyautata dabi`a. Harwayau, ta dalilin karatu na samu buɗe shagon sayar da littattafai na Chapter One.
Yaushe ka fara kirkirar labari da kanka, kuma ko za ka iya tunawa da yadda labarin yake?
E to, tun ina sakandire na fara kwatanta ƙirƙirar labari da kaina, amma bayan na kammala sakandire na shiga jami`a a lokacin ne na fara rubuta cikkaken labari da kaina. Ina aji uku a jami`a na kammala rubuta littafina na farko mai suna Fargar Jaji, labarin soyayya ne.
Kawo yanzu ka rubuta littattafai ko labarai guda nawa?
Na rubuta littattafai da gajerun labaru masu yawa, amma wanda na fitar a yanzu shi ne ‘Husufin Farin Ciki’. Sauran waɗanda na rubuta a baya sun haɗa da ‘Fargar Jaji’, ‘Wankan Wuta’, ‘Rayuwar Rashin Tabbas’, ‘War Haka’, da kuma na Ingilishi mai suna ‘Destiny’s Rage’ da sauransu.
Mene ne ya fi ɗaukar hankalinka wajen rubuta labari, kuma ta ina kake samun ilhamar tsara darussan labaranka?
Abin da yake ɗaukar hankalina wajen rubuta labari shi ne tauraro ko jarumi ko taurarin labarin. Ba na damuwa da jigon labarin fiye da yadda nake damuwa a kan taurarin labarin. Daga taurarin labarin ne nake samun ilhamar yadda labarin ko littafin zai kasance.
Kana cikin waɗanda suka samu nasara a gasar marubuta ta Gusau Institute a shekarar 2019, inda littafin Husufin Farin Ciki ya samu nasara, me ya zaburar da kai ga wannan salon rubutun?
Ka san littafin ‘Husufin Farin Ciki’ gajerun labaru ne, to a haƙiƙa ni gaskiya na shiga gasar Gusau Institute ne saboda buɗe ƙofar da suke yi na yin rubutu a kowanne maudu`i ba tare da faɗa wa marubuci abin da suke son ya rubuta ba, kuma wannan haka ya kamata a ce kowace gasa ta kasance, ba wai a kange marubuci ba a ce masa ya yi rubutu a kan kaza da kaza ba. Asalin marubuci ko fasihi ba ya son a kange shi, sannan a faɗa masa abin da zai yi, idan aka yi haka an tukara tunani da fasahar da ba ta da iyaka.
Ba mu labarin kantin sayar da littattafai na Chapter One, yaya kasuwancin littattafai yake a da da yanzu?
Chapter One ɗan ƙaramin shago ne da aka buɗe domin sayar da littattafai a shekarar 2017, duk littattafan da ake sayarwa babu na karatun makaranta, littattafai ne na zurfafa tunani da ilmin rayuwa da nishaɗi da sauran fannoni na ilimi irin su, rubutattun waƙoƙin Ingilishi, (poetry) falsafa, ayyukan lambu, saƙa, kasuwanci da kyautata dabi`u da sauransu. Kasuwancin littattafai a yanzu yana bunƙasa musamman yadda ake wallafa littattafai masu inganci daga ɓangaren adabin Afirka, akwai shahararrun marubuta irin su Elnathan John, Chimamanda Ngozi Adichie, Abubakar Adam Ibrahim, Ayobami Adebayo, Umar Abubakar Sidi da sauransu, waɗannan marubuta sun ɗaukaka darajar adabin Afirka a idon duniya ta yadda kasuwancin littattafai ya bunƙasa sosai musamman a nan yankinmu na Nijeriya.
Ta yaya za a dawo da dabi`ar son karatu a tsakanin al`ummar Arewa?
A ƙarfafa wa ɗalibai da matasa gwiwa, ƙungiyoyin marubuta su dinga shirya bita da sauran bukukuwa irin na marubuta kamar yadda ake yi a kudu da sauran ƙasashen ƙetare. Gwamnati kuma ta sake inganta ɗakunan karatu. Yanzu gari kamar Kano mai adadin mutane sama da miliyan goma sha shida, bai kamata a ce ɗakin karatu guda ɗaya ba ne a cikin ƙwaryar birnin Kano ba. Kamata ya yi a ce kowacce ƙaramar hukuma tana da nata ɗakin karatun. Wannan, zai sanya dabi`ar karatu a zukatan jama`a.
Yaya kake kallon cigaba ko ƙalubalen da fasahar sadarwa ta zamani ta kawo a harkar sayar da littattafai?
Akwai ƙalubale, sannan akwai kuma cigaba. An samu cigaba ta hanyar sauƙaƙa karatu, inda a yanzu mutane suna samun littattafai na cikin waya da allon kwamfuta. Wasu littattafan suna da tsada, amma zuwan fasahar sadarwa ta zamani ya sauƙaƙa wannan matsalar. Kuma yana kusanta alaƙa a tsakanin makaranta da marubuta. A shekarar 2014 na taɓa samun kyautar littafi na musamman mai ɗauke da sa hannun girma (autograph) daga shahararren marubucin nan ɗan Ingila mai suna Ian McEwan, kuma ta hanyar wannan fasahar sadarwar zamani na samu haka, aka aiko mun da littafin har zuwa gida Nijeriya, ka ga wannan cigaba ne. ƙalubalen da ake samu kuma shi ne ɗauke hankalin mutane daga karatu da wayoyi da sauran shafukan sada zumunta ke yi. Mutane kan ɓata aƙalla awanin uku ko huɗu a waya, alhali za su iya yin amfani da waɗannan lokutan wajen karanta litttafi. Zan iya tunawa a da kafin zuwan wannan fasahar sadarwa, ina iya karanta littafi mai shafi 1000+ a cikin kwanaki goma ko mako biyu, amma a yanzu, irin wannan littafin kan ɗauke ni tsawon wata guda kafin na kammala shi.
Idan ka samu dama wanne abu za ka iya sauyawa a harkar rubutun adabin littafi?
Ga adabinmu na nan Arewacin Nijieriya gaskiya akwai abubuwa da yawa da ya kamata a ce an sauya su. Misali tsarin yadda muke yin rubutunmu, yanayin dab`i da tallata rubutunmu da dai sauransu, dukkansu suna buƙatar canji.
Yaya kake kallon gudunmawar da marubutan Hausa ke bayarwa ga cigaban adabi?
Akwai gudunmawa sosai, domin idan ka kwatanta harshen Hausa da sauran harsuna na gida Nijeriya za ka ga Hausa ta yi nisa sosai wajen kyautata harshe da karatu cikin harshen uwa wanda wannan babbar nasara ce. Harwayau, an samar da rassan adabi irin su waƙoƙi da finafinai da sauransu, sun ginu sosai ta hanyar da har suna samar da kuɗin shiga a cikin al’umma. Wannan babbar nasara ce ƙwarai da gaske.
Bayan karatu da rubutu wane abu ne ya fi ɗaukar hankalinka?
Ina da sha’awar zane-zane da ziyarta wuraren tarihi da kallon finafinan dadaddun al`adu da sauraron waƙoƙin Hausa na zamani, da waƙoƙin ƙasar Indiya da na Amurka irin wanda ake kira da ‘Country music’.
Wacce shawara za ka bayar ga cigaban harkar rubutun adabi a Arewa?
Marubuta su dage su yi karatu sosai, a gane cewa rubutu yana da muhimmanci kuma abu ne mai ɗaukar lokaci, don haka ba ya buƙatar gaggawa. Rubutu kamar girki yake idan har ka yi shi da gaggawa, to ba zai yi daɗi ba. Sannan mu mayar da hankali kan bayyana wa duniya labarunmu na Arewa cikin tsantsar gaskiya ba tare da tsoro ba. Duniya ta san mu a kan gwadaben tsarin al`adunmu ba wai irin yadda ake fassara mu ba.
Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?
Mai haƙuri yakan dafa dutse har ma ya sha romon sa.

