Ka daina yi kamar ƙaramin yaro don ba a ba ka minista ba – Fadar Shugaban ƙasa ga El-Rufa’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya shawarci tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i da ya daina nuna halin yara kaɗai saboda bai samu muƙamin minista ba.

Da farko dai, Shugaba Tinubu ya sanya sunan El-Rufa’i acikin waɗanda aka so bai wa minista a gwamnati, wanda daga bisani Majalisar Dattawa a yayin tantancewa ta cire shi.

Daga lokacin ne El-Rufa’i ya zama ƙarfen ƙafa ga Gwamnatin Shugaba Tinubu da jami’iyyar APC ta hanyar soka da wasu ayyuka na nuna fushi.

A kwanan nan ne aka yi hira da El-Rufa’i, a inda ya yi ikirarin cewa ba majalisar ba ce ta ƙi amincewa da shi, Shugaba Tinubu ne da kansa.

Saidai, a yayin hira da gidan talabijin na ‘channels’, Onanuga a ce duk da cewa El-Rufa’i ya yi ƙoƙari matuƙa wajen kai Tinubu ga nasarar zama Shugaban ƙasa, ba dalili ba ne da zai cigaba da nuna fushi don bai zama minista ba.

Ya ce, har yanzu Fadar Shugaban ƙasa tana alfahari da ƙoƙarin da ya yi wajen kafa gwamnatin Shugaba Tinubu.

Ya ƙara cewa, Tinubu ba ya adawa da tsohon gwamnan Kadunan, amma kuma shi duk inda ya je ƙoƙarin nuna adawarsa ya ke akan Shugaban ƙasar saboda raɗaɗin rasa muƙamin.

Onanuga ya yi kira ga El-Rufa’i da ya kawar da kai game da lamarin kasancewarsa mutumin da ke yi wa ƙasa hidima tun daga 1999 kuma ɗaya daga cikin manyan ƙasa.

By Babaji