Gwamnatin Sokoto za ta kashe miliyan N998 a shirin ciyarwa na Ramadan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce za ta kashe kimanin Naira miliyan 998 a shirin ciyarwa a yayin azumin watan Ramadana na shekarar 2025.

Za a gudanar da shirin ne a cibiyoyi 155 dake sassan jihar.

A lokacin da ya ke magana a yayin raba kayan abinci ga manajojin cibiyoyin, Gwamna Aliyu Ahmad ya ce za a bai wa kowacce cibiya ɗanyen abinci kala-kala da kayan girke-girke.

Ya ce, mutane 1,400 aka ɗauka a matsayin waɗanda za su gudanar da ayyukan ciki har da mata masu girki guda 610.

Ya kuma ce, za a riƙa ciyar da aƙalla mutane 20,000 a kowacce cibiya a kullum tun daga farkon watan har zuwa ƙarshe.

Haka kuma gwamnan ya sanar da cewa an raba wa malaman addini 2,400 buhunan masara 990 a ƙarƙashin wani shirin na tallafin Ramadana.

Kowane limami an ba shi buhu biyar na masara da N100,000 yayin da na’ibansu kuma suka samu buhu uku-uku da N50,000 ga kowannen su. Kowane ladani kuma ya samu buhu biyu na masara da N50,000.

Har’ilayau, Gwamna Aliyu ya ce an ba kowane ɗaya daga cikin malamai 300 daga gundumomin N200,000, yayin da aka bai wa wasu malaman kuma dubu ɗari-ɗari.

Haka ma malaman zaure daga kowacce gunduma na ƙananan hukumomi 23 na jihar, waɗanda kowannen su za a ba shi N50,000.

Gwamna Ahmad ya ce, sun ɗauki matakin inganta malaman ne don su cigaba da bai wa addini gudunmawa.

By Babaji