Babu shirin cire Ganduje, yayin da El-Rufai ya ƙaurace wa taron jagororin APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugabancin jam’iyyar APC ya yi watsi da zargin da ake yi na cewa akwai yiwuwar Shugaba Bola Tinubu ya nemi Abdullahi Umar Ganduje da ya yi murabus daga kujerar jagorancin jam’iyyar a zaman jagororinta a Abuja, ranar Laraba.

Sakataren jam’iyyar, Sanata Ajibola Basiru ya bayyana hakan a yayin hira da ƴan jarida, inda ya bayyana zargin a matsayin ƙirƙirarre da ba shi da tushe.

Ya ce, zaman nasu ba zama ne na zaɓe ba, wanda sun so gudanarwa tun wata Satumbar 2024, don haka babu maganar sauke Ganduje ko neman ya yi murabus.

Sanatan ya kuma ce, a taron za su bada rahoton mambobi masu rajista da kuma nasarorin da aka samu acikinta.

Kazalika, ya ƙara da cewa, zaman zama ne da ya ƙunshi tattauanawa da jagorori da masu-ruwa-da-tsaki wanda shi ne jigon ajandodinsa.

Saidai, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya sanar da cewa ba zai halarci taron jagororin ba, wanda daga cikin akwai Shugaba Tinubu, kamar yadda ya bayyana a wata hira da gidan telebijin, ranar Litinin.

Ya ce, ba a ba shi saƙon gayyata ba, hasali ma shi zai je ƙasar Misra ne a ranar taron.

By Babaji