Gwamnatin Abba za ta gina tsangayoyin almajirai 44 a Kano – Gwani Falaki

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

An bayyana cewa a ƙoƙarinsa da yake yi wajen cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe ta fuskar bunƙasa ilimi da taimakon addini ga ɗaukacin al’ummar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin cewa zai bunƙasa ilimi da kuma inganta rayuwar al’umma ta kowace fuska, yanzu haka wannan ya yi nisa wajen cika alƙawari kamar yadda ko wanne mutumin kirki ya yi alƙawari ya ga ya cika ba yaudara ba, to ba shaka kowa shaida ne a Kano Gwamna Abba, na cika alƙawarin Kanawa, har ma wanda bai alƙawarin yi ba a lokacin yaƙin neman zaɓe, kamar dai yadda mai bai wa Gwamna shawara kan harkar tsangayu da almajirai Gwani Musa Falaki ya bayyana ga ‘yan jarida a wani taro na ƙaddamar da raba kujeru sama da dubu 70 da gwamnan ya ƙaddamar a filin kasuwar Bajekuri a Juma’ar da ta gabata a birnin Kano.

“Gwamna Abba Kabir Yusuf, shi ne gwamna da ya ware sama da kaso 30 cikin 100 a kasafun kuɗi na 2023 zuwa 2024 wanda shi ne gwamna na farko a Kano ko ma a ce a ƙasa baki ɗaya da ya yi wannan bajinta, don haka gwamna ya cancanci yabo wajen nuna kishin Jihar Kano da al’ummarta.”

Gwani Musa Falaki, ya ce “a ɓangaren ofishina na tsangayu da almajirai gwamna ya yi alwashin gina tsangaya ta zamani a ko wacce ƙaramar hukuma ta Kano domin bunƙasa ilimi da haddar Alƙur’ani.

“Haka kuma ga yunƙurin samar da banɗakuna 15 da rijiyar burtsatse a manyan tsangayoyi 20 na Kano ga kuma taimako da gudumawa da ya bayar a zamanin azumin Ramadan da ya gabata inda aka ciyar da almajirai kimanin dubu 9 a abinci mai inganci ga kuma hidima ta ba da sabulon wanki da wanka ga almajirai da hidima da aka yi wa malamai bayan kammala azumin watan Ramadana na ɗanyar shinkafa da dai sauran gudunmawa ta abin buƙata da gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir ta bayar.

“Don haka akwai buƙatar yi wa gwamna addu’a don cigaban Kano wajen zaman lafiya arziƙi da dai sauransu,” inji shi.

By ukarofi