Gwamnatin Kano na duba yiwuwar samarwa da ƴan soshiyal midiya damar yin Difloma

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano za ta duba yiwuwar haɗa kai da Jami’ar Bayero, Kano, domin bai wa masu yaɗa aiyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf a kafafen sada zumunta damar yin difloma don inganta aikin na su.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a yayin bikin rufe taron ƙarawa juna sani na yini biyu da Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta shiryawa yan soshiyal midiya .

Kwamared Waiya ya bayyana cewa, idan matasan suka sami damar yin kwas din zai ƙara musu damar yin amfani da kafafen sada zumunta yadda ya kamata wajen yaɗa bayanai da manufofi da ayyukan gwamnatin Kano.

Kazalika, ya ƙara da cewa gwamnatin jihar tana ɗaukar yan soshiyal midiya a matsayin jakadunta, don haka ya buƙace su da su kasance masu yaɗa ayyukan gwamnatin Kano ba wai cin mutuncin mutane ba.

Waiya ya ce akwai buƙatar yan soshiyal midiyan su riƙa gudanar da bincike don ribatar damammakin kasuwanci da ake da su a shafukan sada zumunta don su zamo masu dogaro da kawunansu.

A jawabinsa na godiya, Shugaban ƙungiyar masu yaɗa ayyukan gwamnatin Kano a Twitter ya yabawa ma’aikatar yaɗa labarai da harkokin cikin gida bisa shirya taron, wanda ya basu damar samun ƙarin ƙwarewa da ilimi domin inganta yaɗa ayyukan gwamnati.

A wata sanarwa da daraktan ayyukan na musamman ga ma’aikatar yaɗa labarai Sani Abba Yola ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24, ya ce a yayin taron malamai da dama sun gabatar da ƙasidu da dama.

Yayin taron dai, mahalarta taron sun bayar da lambar yabo ga Kwamishinan bisa la’akari da yadda ya himmatu wajen ganin an yaɗa ayyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf bisa ƙwarewa da ilimi.

By ukarofi