Gwamnan Kano ya ƙaddamar da jigilar alhazan farko na Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, a yau Laraba ya ƙaddamar da jirgin farko na Alhazan Jihar Kano da za su gudanar da aikin Hajji na bana.

Gwamna Abba Kabir Yusif, wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta, ya shawarci Alhazan da su kasance jakadun kirki na Jihar Kano tare da yin addu’a domin zaman lafiya, cigaba da haɗin kan jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

A jawabin sa, Kwamared Aminu Abdussalam ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na tallafawa dukkanin Alhazan da ke shirin gudanar da ibada a ƙasa mai tsarki tun daga tafiya har zuwa dawowarsu lafiya.

Tun da farko, mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya shawarci alhazan da su kasance masu nutsuwa, da bin doka da oda yayin gudanar da ibadar. Ya kuma yi addu’a ga Allah da ya kare su daga tafiya har zuwa dawowa.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Sulaiman A. Dederi ya fitar, ya bayyana cewa, daraktan hukumar jin daɗin Alhazai na Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya ce jirgin farko ya ƙunshi alhazai daga ƙananan hukumomi goma sha daya 11 da suka haɗa da:

Ajingi LGA: Alhazai 15 (Maza 10, Mata 5)
Tofa LGA: Alhazai 17 (Maza 12, Mata 5).
Tudun Wada LGA: Alhazai 115 (Maza 84, Mata 31).
Doguwa LGA: Alhazai 94 (Maza 73, Mata 21).
Bebeji LGA: Alhazai 82 (Maza 67, Mata 15).
Garin Malam LGA: Alhazai 47 (Maza 33, Mata 14).
Gaya LGA: Alhazai 14 (Maza 10, Mata 4).
Madobi LGA: Alhazai 36 (Maza 21, Mata 15).
Kabo LGA: Alhazai 18 (Maza 13, Mata 5).
Wudil LGA: Alhazai 36 (Maza 30, Mata 6).
Rimin Gado LGA: Alhazai 33

Kazalika, jami’an gwamnatin Kano 15 da jami’an hukumar na ƙasa 10 ne ke tare da alhazan domin sa ido da jagoranci akan harkokin ibada.

Jimillar alhazai 560 ne aka yi jigilar su a cikin jirgin kamfanin Max Air zuwa Filin Jirgin sama na Prince Mohammed Bin Abdulaziz da ke Madina, wanda ya tashi da ƙarfe 12:11 na rana yau.

Alh. Lamin Rabi’u Danbappa ya kuma jaddada cewa gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif ta samar da dukkanin kayan buƙata da tsare-tsaren da suka dace domin tabbatar da jin daɗi, tsaro da walwalar alhazan.

An samu halartar manyan jami’an gwamnati a wannan taron, ciki har da shugaban hukumar kula da Alhazai, Alhaji Yusif Lawan, mambobin hukumar, kwamishinoni da masu ba wa gwamna shawara na musamman.

By ukarofi