
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, matakai masu tsauri da muhimmanci da Shugaba Bola Tinubu ke ďauka, su ne suka dace tsarin tattalin arziƙin ƙasa domin amfanin kowane ďan Nijeriya.
Shettima ya bayyana hakan ne a taron lakcar injiniyoyi na ‘Mechanical Engineering Distinguished Lecture’ karo na 15 da aka gudanar a Abuja, ranar Laraba.
Ya ce, gwamnatin Tinubu tana ɗaukar haraji na daidai don ciyar da ƙasar gaba, lamarin da ya aka gabatar da kudiringyaranharajia shekarar da ta gabata.
Haka kuma ya bayyana aikin injiniyoyi ta hanyar amfani da na’urorin zamani a matsayin abinda zai samar da kyawawan sakamako don al’umma da ci-gaban ƙasar.
Shettima ya kara da cewa, gwamnatin tana aikin ne tukuru wajen ganin ta samar da ababen more rayuwa masu dorewa a kowane fanni musamman wajen bunkasa harkokin tattalin arziƙi, lamarin da ya sa suke ɗaukar matakan da suka dace na gina ƙasar a zamanance.
A nasa jawabin, Shugaban taron, Cif Bisi Akande ya bayyana tasirin injiniyanci ga ci-gaban ƙasa, inda ya yi kira ga shugabanni da su ďore akan kokarinsu na kula da bangaren da kwarkwasa.
Ya kuma ce, lallai fasahar zamani tana da tasiri ga harkar injiniyanci, yana mai kira ga injiniyoyi da su rika amfani da ci-gaban wajen inganta ayyukansu.
