Isra’ila ta maida martani kan Houthi

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Houthi dai ta kasance kan gaba a labarun da su ka shai gabar ta tsakiya musamman tun yaƙin basasar Yaman a 2014 da hakan ya kawar da marigayi shugaba Ali Abdallah Saleh daga karagar mulki wanda ya kai ma ga kashe shi a wani yanayi na kaskanci. Houthi wacce kungiyar ‘yan shia ne da kuma ba mamaki ta ke samun goyon bayan ƙasar Iran. Haƙiƙa matakin da ta ɗauka na marawa Hamas baya kan Isra’ila a yaƙin Gaza ya ja ma ta jakar tsaba. Gaskiya in ka debe Hezbollah a Lebanon ba wata ƙungiya da ke da makamai a nan gabar ta tsakiya da ta fito ƙarara ta ƙalubalanci Isra’ila kan zubar da jinin Falasɗinawa a Gaza kamar Houthi. Lallai Houthi ta ba da gudunmawa mai yawa ta fannin mara baya da ƙarfafawa Falasɗinawa ko al’ummar Gaza gwiwa cewa ba duk duniya ce ta yi biris da su ba. Hakan ya sa a lokacin Houthi ta dau matakin kai hare-hare kan jiragen ruwan dakon man fetur na ƙasashen yamma musamman Amurka da Burtaniya da duk ma dai masu marawa Isra’ila baya da ke zirga-zirga a Bahar Maliya. Daura damarar hare-haren ko kai tsaye ba su wargaza wasu jiragen ruwan ba amma hakan ya haddasa cikas da firgici ga ƙasashen da abun ya shafa. Ba wata-wata sai a ka ga Amurka da Birtaniya da a baya ba sa takurawa Houthi kan mamaye sassan Yaman sun ƙaddamar da miyagun hare-hare kan yankunan da Houthi ke jagoranci a cikin Yaman ɗin da su ka hada da babban birnin kasar San’a’a. Gomman mutane sun rasa ran su sanadiyyar hare-haren na waɗannan wasashen Yamma biyu duk da a baɗini ba wai su na son kawar da Houthi daga jagoranci ba ne don ba wa zaɓaɓɓiyar gwamnatin birnin Aden na kudanci galaba. Siyasar duniya na taka rawa a nan don su ma Houthi a wani ɓangaren su na da amfani ga musamman yammacin duniya don barazana da su ke yi wa Saudiyya da tsoron ƙarfafa tasirin Iran da hakan kullum dole ya sa Saudiyya ta riƙa neman goyon bayan su da sayan makamai a wajen su. Sulhun da ƙasar Sin ta cimma nasarar jagoranta da ya dawo da diflomasiyyar Saudiyya da Iran ya rage ko ma ya dakatar da hare-haren Houthi kan Saudiyya ba ma irin garuruwan kudancin ta kamar Najran. Tabbas yammacin duniya ba za su iya jagorantar wannan sulhun ba don ba ribar da hakan zai sama mu su. 

Gwamnatin Isa’ila ta tabbatar da kai harin makami mai linzami kan babban filin saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke Tel Aɓiɓ.

Wannan shi ne karo na farko da makami da Isra’ila ta ce daga Yaman a ka cillo shi ya sauka a tsakiyar ƙasar.

Hakan ya nuna ƙungiyar mayakan Houthi na Yaman ne su ka habo makamin a cigaba da cijewa da su ke yi wajen nuna marawa Hamas baya a yaƙin Gaza.

An ga jami’an na tsaye a bakin wani katon rami da makamin ya tona a cikin babban filin jirgin da hakan kazalika ya raunata mutum 6 da kuma tilasta dakatar da tashin wasu jirage.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dau alwashin rama wannan hari kan houthi har ma da Iran da ya ke cewa na mara ma ta baya.

Wannan ya zo ne gabanin gaiyato dubban sojojin Isra’ila masu jiran kira don kara matsa lambar hare-hare don murkushe Hamas a Gaza.

Isra’ila ta kai hare-hare da jiragen yaki kan sassan Yaman da ke hannun ƙungiyar Houthi da dama ita ke riƙe da babban birnin ƙasar San’a’a.

Harin ya shafi yankin Hodeida ne mai tashar teku inda Isra’la ta ce ta nan ne Iran ke turo makamai ga Houthi.

Isra’ila ta kai harin ne don ramuwa ga harin makami mai linzami da Houthi ta kai ya faɗa kan babban filin jirgin saman Ben Gurion da ke Tel’aɓiɓ.

Houthi ta tabbatar da harin da zargin cewa har da haɗin gwiwar Amurka a wajen farmakin duk da majiyar Amurka ta musanta hannun.

Houthi ta ce mutum 21 sun samu raunuka a sanadiyyar hare-haren na Isra’ila.

Houthi ta ce za ta kai hare-hare da za su datse harkokin samaniyar Isra’ila musamman hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da ya ke mafi girma a kasar.

Don haka yanzu kamar hare-hare za su iya tsananta tsakanin Isra’ila da Houthi amma an samu alamun dakatawar nan farmakin Amurka kan Houthi bayan kashe gomman mutane a Yaman ɗin da Amurka ta yi.

Da alamu Amurka da kungiyar Houthi ta Yaman sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Mai shiga tsakani don sulhu wato kasar Oman ta ce sassan biyu sun amince da dakatar da kai wa juna hari inda Houthi ta yi alƙawarin daina kai hare-hare ga jiragen ruwan ƙasashe masu marawa Isra’ila baya da ke hada-hada a Bahar Maliya.

Shugaba Trump na Amurka ya tabbatar da sulhun da nuna Houthi ta janye kai wa jiragen dakon mai hari don Amurka ta daina kai ma ta hare-haren boma-bomai.

Da alamu Houthi ba za ta iya jure dogon yaki da Amurka ba amma hakan ba lallai ya na nuna kungiyar ta daina goyon bayan Hamas ba ne.

Gaskiya martanin da Isra’ila ke kai wa kan duk kungiyar da ta nemi ƙalubalantar ta kan Hamas ba ya karewa don Isra’ila kan cigaba dakai hare-hare a duk lokacin da ta ga dama. Ga ma ƙasar Sham duk da kawar da gwamnatin Bashar Al’Asad har yanzu Isra’ila na cigaba da kai hare-hare da sunan farautar mayaƙan da Iran ke daukar nauyi a kasar. Sabon shugaban Sham din Ahmad Al-Sharaa ya bukaci sa bakin ƙasashen duniya don dakatar da Isra’ila amma har yanzu ba a kai ga nasara ba. Daidai wannan lokaci sai ma ƙara taƙarƙarewa da Isra’ila ke yi don mamaye dukkan yankin Gaza.

Wani mummunan harin da Isra’ila ta kai yankin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16.

Rundunar kiyaye farar hula ta Gaza ta bayyana cewa harin ya shafi matsuguni ne a Al-mawasi da ke garin Khan Younis na kudancin Gaza.

Jagoran rundunar ta kare farar hula a Gaza Mahmud Bassal ya ce cikin waɗanda a ka kashe akwai mata 7 da kananan yara.

Da a ka tuntuɓi rundunar sojan Isra’ila don ƙarin bayani ta ce ta na tattara bayanai ne tukun.

Zuwa yanzu daga fara yaƙin Gaza a Oktobar 2023  Isra’ila ta yi sanadiyyar kashe Falasɗinawa 52,535.

A cigaba da hare-hare da Isra’ila ke kara kai wa Zirin Gaza, a yanzu ta yanke matsayar mamaye yankin gaba daya.

A cikin tsarin akwai ba da dama ga al’ummar yanzin su zaɓi a kaurar da su zuwa kudancin zirin da ya shafi yankin Rafa.

Wannan na zuwa ne bayan Isra’ila ta kira dubban sojojin da ke zaman jira don cimma wannan muradi.

Shugaban Amurka Donald Trump wanda dama ke buƙatar lallai Gazawa su bar yankin na su ya yi alwashin taimakawa da abinci amma bai yi wani sharhi kan ruwan boma-bomai da Isra’ila ke yi a yankin ba.

ƙungiya taraiyar turai ta nuna damuwa cewa matakin kawai zai kara kawo asarar rayuka ne.

An shafe fiye da wata biyu Isra’ila ta hana kayan agaji shiga yankin Gaza da hakan ya jawo matsanancin yanayi buƙatar kayan tallafi.

Kammalawa;

Duk da Saudiyya ta sake nanata matsayar ƙin lamuntar mamaye Gaza da Isra’ila ke yi hakan ba zai hana Isra’ila yin abun da ta ga dama ba. Kimanin mutanen Isra’ila 21 da ke hannun Hamas ya sa ma ba ta jefa boma-bomai na kan mai uwa da wabi ba a Gaza. Akwai buƙatar Masar da Katar su sake yunƙurowa don shiga tsakani kafin kisan ƙare dangi na haƙiƙa ya wakana a Gaza

By ukarofi