JAMB ta sake shirya jarrabawa ga ďaliban da suka samu tsaiko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Haďaka ta bada Gurbin Karatu ga Dalillbai (JAMB), ta sanar da sake tsara sabon jarrabawar UTME ta 2025 ga dalibai 379,997 a Jihar Legas da wasu jihohi biyar daga Kudu maso Gabashin Nijeriya da suka samu matsalar sadarwa a yayin jarrabawar a karon farko.

Rajistiran Hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede a taron manema labarai, a ya karbi laifin kurakurai da aka samu a lokacin rubuta jarrabawar a karon farko, ranar Laraba.

Ya tabbatar da cewa, za su sanar da ďaliban da lamarin ya shafa ta sakonnin kar ta kwana (SMS) a ranar Alhamis ta yadda za su samu damar sake ciro takardar bayanan jarrabawarsu da za a sake yi a ranakun Juma’a da Asabar.

Ya bayyana cewa, tsaikon da aka samu wanda ya haddasa matsaloli ga ďaliban, ya faru ne sakamakon rashin isar da sakon damar rubuta jarrabawar daga ďaya daga cikin na’urorin sabis ďin JAMB.

Hukumar ta ce, kimanin sakamako 1,955,069 ne aka yi aiki akansu, inda guda 4,756 ne kacal suka samu maki 320 zuwa sama, wato kaso 0.24.

Haka kuma guda 7,658 sun samu maki 300 zuwa 319, wanda ke wakiltar kaso 0.39, lamarin da ya bada jimillar waɗanda suka samu maki 300 zuwa sama ya kai 12,414.

Sai kuma dalibai 73,441, waɗanda suka samu maki 250 zuwa 299 da kuma guda 334,560 da suka ci 200 zuwa 249.

By Babaji