Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
A kokarinta na tabbatar da ɗa’a tare bin doka sau da ƙafa, hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano a yau ta tsayar da matsaya kan bikin nan da ƴan mata ke Sanya ƙananan kaya tare da yin rawar nuna fitsara wato ƙauyawa day, in da ta haramta shi. haka kuma, hukumar ta sanar da dakatar da dukkannin ɗakunan taro da gidajen biki na musamman wato Event centers har zuwa lokacin da za’a cimma matsaya kan dokokin da aka ɗora musu domin kawo tsafta tare da tabbatar da ba a saɓawa ƙa’idar addini ba ko kuma cin mutuncin al’ada.
Shugaban hukumar tace fina-finai Abba El-mustapha ne ya bayyana hakan a yau Asabar a yayin wata ganawa ta musamman da manema labarai jim kaɗan bayan wani taron gaggawa da hukumar ta gabatar da manyan ma’aikatanta a kan al’amarin na bikin ƙauyawa day.
Ta cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar tace finafinai da ɗabi’a ta jihar Kano Abdullahi Sani Sulaiman ya ce, shugaban hukumar ya ƙara da cewa, wannan mataki ya zama dole la’akari da ƙorafe-ƙorafe da hukumar ke karɓa tare da jan hankali daga malamai tare da wasu masu faɗa a ji a faɗin jahar Kano.
El-mustapha, ya bayyana cewa wannan matakin an ɗauke shi ne bisa ƙa’ida kasancewar doka ce ta bawa hukumarsa damar ɗaukar mataki kan duk wani mai kiɗan DJ, ko masu ɗakunan taro da gidajen bikin na musamman wato event centers tare da damar saka ido a duk wani biki da ake gudanarwa a faɗin Jihar Kano matsawar za’a saka kiɗa ko waƙa.
Kazalika El-mustapha ya ce dangane da wannan mataki hukumarsa ta shirya tsaf domin ƙara haɗa hannu da jami’an tsaro na farin kaya, ‘yan sanda, hukumar Hisbah da kuma ‘yan vigilante wato ‘yan ƙato da gora tare da sauran dattawan unguwanni da kuma ƙungiyoyin matasa a Jihar Kano domin tabbatar da an kawo ƙarshen wannan rashin ta ido da ke damun al’umma.
