Gwamnatin Kano ta musanta rahoton hana gudanarwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ke ikirarin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci a rufe hukumar gudanarwar harkokin gwamnati a jihar.

A sanarwar da Sakataren yaɗa labaran gwamnatin, Musa Tanko Muhammad ya fitar, gwamnatin ta ce umarnin na wucin-gadi ne kuma matakin kariya ne da aka ɗauka bisa tsare-tsaren gudanarwar kuɗaɗe.

Ya ce, an bada umarnin, wanda ya dakatar da shigar da takardu a ofishin gwamna, an fitar da shi ne tun a ƙarshen watan Disambar 2024 lokacin da kasafi ke karewa da kuma lokacin da aka miƙa na 2025 ga majalisar dokoki.

Ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne domin kauce wa kashe-kashe ba bisa ƙa’ida ba da tabbatar da bin dokokin kuɗaɗe, yana jaddada cewa babu kuɗaɗe da za a amince da fitar da su ba tare da sahalewar doka ba.

A cewar sanarwar, ayyukan hukumomin gwamnati kamar su tsaro, lafiya, ilimi da kula da muhalli suna gudana ba tare da tsaiko ba saboda ƙoƙarin gwamnati wajen kula da harkokin jihar.

By Babaji