
Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taron ‘Sustainability Week a birnin Abu Dhabi na ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya cimma muhimmin yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Nijeriya da UAE, tare da ƙulla sababbin haɗin gwiwa a fannin sauyin yanayi.
Rahotanni sun bayyana cewa, bayan kammala taron a Abu Dhabi, Shugaba Tinubu ya tsaya a birnin Paris na Faransa domin gajeren hutu kafin komawarsa gida Nijeriya.
Daga cikin nasarorin ziyarar akwai ƙarfafa dangantakar tattalin arziki, janyo zuba jarin waje, da kuma haɗin kai kan shirye-shiryen kare muhalli da ci-gaba mai ɗorewa.
Ana sa ran dawowar shugaban ƙasar zai ƙara zafafa tattaunawa da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma, musamman waɗanda ke da alaƙa da kasuwanci, makamashi, da sauyin yanayi.
