Gwamnatin Kano ta sanar da janye dokar hana fita

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya umarci kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano da ya janye dokar hana zirga-zirga da aka sa biyo bayan sanar da hukuncin kuton sauraren zaɓen Gwamnan jihar Kano.

Da yake sanar da umarnin, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya ce za a janye dokar ne saboda zaman lafiya da aka samu a jihar.

Ya ƙara da cewa, janye dokar zai ba wa al’umma damar ci gaba da gudanar da alamuransu na yau da kullum kamar yadda aka saba.

“Janye dokar za ta bai wa zai bawa al’ummar Kano damar gabatar da Sallar Juma’a cikin nutsuwa,” in ji shi.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta sanar da ɗage dokar hana fita ta tsawon sa’a 24, da aka sanya a jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdulahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da haka a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook.

A ranar Laraba ne dai rundunar ƴan sandan Kano ta sanya dokar hana fita tun bayan yanke hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna, da ya soke nasarar Engr. Abba Kabir Yusuf, tare da ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen gwamna.

A zagayen da Manhaja ta yi a cikin birnin Kano ya nuna cewa jama’ar Kano sun bi wannan umurni na hana fita, ta yadda al’umma suka zauna gida ba tare da fita ba.