Daga RABIU SANUSI
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da sabbin tsauraran matakai domin tafiyar da bukukuwan hawan Sallah, biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da yiwuwar wasu su tayar da tarzoma da kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, ya ce matakin ya biyo bayan bayanan tsaro da majalisar tsaron jiha ta bayar wanda ke nuna cewa wasu na shirin haddasa ruɗani a lokacin bukukuwan.
Ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jajircewa wajen kare al’adun gargajiyar Kano, amma ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ba.
Sanarwar ta ce bayan tuntuɓa da sauran masu ruwa da tsaki, an amince da wasu tsare-tsare na gudanar da bukukuwan.
Za a gudanar da hawan Idi ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II daga filin Idi na Ƙofar Mata, ta bi hanyoyin da aka tanada zuwa Gidan Shettima, sannan a kammala a Ƙofar Fatalwa da ke fadar Sarkin Kano.
Hawan Nasarawa zai gudana ne cikin sabon tsari ba tare da amfani da dawaki ba, yayin da aka dakatar da Hawan Daushe zuwa wani lokaci na gaba.
Haka kuma an dakatar da Hawan Fanisau da Hawan Ɗorayi domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Gwamnatin ta umurci jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen sa ido tare da tabbatar da bin dokokin da aka gindaya tare da ɗaukar duk matakan da doka ta tanada kan duk wanda ya karya doka.
An kuma buƙaci al’umma da su kasance masu bin doka da oda, su guji yaɗa jita-jita, tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai domin tabbatar da gudanar da Sallah cikin lumana.
Gwamnatin ta yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro wajen tabbatar da tsaro a jihar, tare da jaddada ƙudurinta na ganin an gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali.
Daga ƙarshe ta taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar Sallah tare da fatan alheri da zaman lafiya.
