Gwamnatin Kano ta wanke Ado Doguwa daga zargin kisan kai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta ce binciken da ta gudanar kan tuhumar da ake yi wa ɗan majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa kan laifin kisan, ya nuna cewa ba a same shi da laifin da ake zargi ba.

Lokacin da ya yi wa manema labarai bayani, kwamishinan shari’a na jihar Kano, Lawan Musa Abdullahi ya ce an samu saɓani da dama cikin bayanan da aka samu daga wurin shaidu.

Ya ƙara da cewa a yayin da suke gudanar da bincike sun gano cewa ma’aikatan asibiti ba su yi cikakken bincike kan mutanen da ake zargin an harba da bindiga ba, soboda haka ba a iya tabbatar da cewa an harbe su ba.

Kwamishinan ya ce an gudanar da bincike kan bindigogi da harsashai da ke hannun ‘yan sandan da ke tare da ɗan majalisar a lokacin da rikicin ya faru.

Sai dai a bayanin nasa babu wata shaida da ta nuna cewa an yi amfani da bindigogin, kasancewar jami’an ƴan sandan sun mayar da daidai adadin harsasan da ke a hannunsu.

A ranar 1 ga watan Maris ne, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta gurfanar da ɗan majalisa Alhassan Ado Doguwa a kotun majistre bisa zargin harbin mutum uku a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki na tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu.

An tuhumi ɗan majalisar tare da wasu mutum 13 da hannu a kisan kai da janyo jikkatar mutane sakamakon harbi.

Kotun a ƙarƙashin shugabancin alkali Ibrahim Yola ta umurci da a tsare dan majalisar a gidan yari kafin ta saurari buƙatar nema wa ɗan majalisar beli a ranar 7 ga watan Maris.

Lauyan dan majlisar ya nufi babbar kotun tarayya a ranar 6 ga watan na Maris inda ya ƙalubalanci hurumin kotun majistre na sauraron karar. Babbar kotun a ƙarƙashin alkali Yunusa Muhammad ta bayar da belin ɗan majalisar kan kudi naira miliyan 500.

Babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Litinin din da ta gabata ta bayyana tuhumar dan majalisar da aka yi da aikata laifuffukan kisan kai a matsayin matakin da ya sabawa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Da yake yanke hukunci a kan buƙatar da Doguwa ya shigar ta tauye masa hakki da kuma tsare shi ba bisa ka’ida ba da qaramar kotun ta yi, mai shari’a Alƙali Mohammed Yunusa ya ce babbar kotun majistre ba shi da hurumin sauraron kararrakin da ke da alaka da zargin da ake yi wa dan majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *