Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, za ta fara gurfanar da duk masu ƙin biyan ƙuɗaɗen haraji a shekarar 2025, a wani ɓangare na sauye-sauyen da ta ke yi a harkokin haraji.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Blueprint Manhaja daga Jihar Kaduna a ranar Asabar.
A cewar sanarwar, Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta Jihar Kano (KIRS), Dr. Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi ga Gwamnan Jihar a wani ɓangare na bita da gwamnatin jihar kano ta shiryawa manyan jami’anta.
Dr. Zaid Abubakar ya fayyace cewa za ai hakan ne ba wai don ƙara haraji ba, illa dai don inganta ayyukan tattara kuɗaɗen haraji da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin haraji.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar ta yi hasashen samun kuɗaɗen haraji sama da naira biliyan 20 a kowanne zango na shekarar 2025.
Ko a baya bayan nan ma dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke tsohon shugaban hukumar tara kuɗaɗen haraji ta jihar tare da naɗa sabo, wanda hakan ya taimaka wajen ƙara inganta ayyukan hukumar a Zango na uku da na huɗu na shekarar 2024.
Kazalika waɗannan gyare-gyare anyi su ne don tabbatar da kuɗaɗen harajin jihar Kano ba su zurare ba.
