
Daga BELLO A. BABAJI
Ƴan kasuwar man fetur daga matatar Ɗangote sun rage farashin lita daga N1,060 zuwa N939.50.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gidajen mai ciki har da MRS sun rage farashin litarsu a ranar Juma’a.
Gidan man MRS dake Ojota a Legas su na sayar da lita a N939.5.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan da Kamfanin Ɗangote ya sanar da rage farashin lita daga N970 zuwa 899.5 don sauka ga al’umma yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan ƙarshen shekara.
Kamfanin ya kuma sahale wa kowane kwastoma sayan mai a bashi na adadin da ya saya kuɗi a hannu ta bankunan Access, First da Zenith.
