Amurka ta kashe jagoran IS a Siriya yayin wani hari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Amurka ta ce kashe jagoran ƙungiyar IS, Abu Yusif a ƙasar Siriya.

Dakarun Amurka na (Centcom) sun ce sun kai farmaki ne ta sama inda suka nufi Abu Yusif a yankin gabashin ƙasar.

Jami’an Amurka sun ce sun kuma kashe wani wani mamban IS.

An kai harin ne a wani yankin dake ƙarƙashin mulkin Siriya da jami’an Rasha.

Kwamandan Centcom, Janar Michael Erik Kurilla ya ce Amurka da ƙawayenta dake aiki a yankin ba za su bar ISIS su yi amfani da damar halin da ƙasar take ciki.

IS ta na yunƙurin fasa wajen da aka tsare mambobinta 8,000 a Siriya, inda ya ce su na ƙoƙarin dakatar da hakan da wasu hare-hare da ƙungiyar ke shirin kai wa ƙasar a ciki da wajen ta.

By Babaji