
Daga BELLO A. BABAJI
An sako tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello daga gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja bayan cike ƙa’idodin beli da Babbar Kotun Tarayya ta gindaya masa.
Kakakin Hukumar Gyaran hali (NCoS) na Abuja, Adamu Duza ya bayyana hakan inda ya ce an sako tsohon gwamnan ne a yammacin Juma’a.
A baya ne Alƙalin Maryanne Anenih ta yi hukuncin belin Yahaya Bello akan Naira miliyan 500 da kuma mutum uku da za su tsaya masa dake da kadarori a Maitama ko Guzape ko kuma Asokoro duk a Abuja.
Kotun ta kuma umarci Bello da ya bayar da fasfo ɗinsa da kuma taiƙace masa tafiye-tafiye a wajen Nijeriya ba tare da izini ba.
