Kotu ta haramta zaɓukan mazaɓu na APC a Jihar Ribas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babbar Kotun Jihar Ribas dake Fatakwal ta haramta zaɓukan ƙananan hukumomi da na jiha da jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Tony Okacha ta shirya.

APC reshen jihar ta gudanar da zaɓukan duk da hukuncin kotun na haramta yin hakan ƙarƙashin Okocha.

A ranar 14 ga watan Disamba ne Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin jagorancin jam’iyyar reshen jihar.

Wasu mambobin jam’iyyar sun shigar da ƙara, a inda suka yi zargin cewa an ware su cikin harkokin jam’iyyar.

By Babaji