Gwamnatin Katsina ta bada tallafin N38m ga iyalan waɗanda ta’addanci ya rutsa da su a Musawa da Sabuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙoƙarinsa na yaƙi da da ta’addanci, fashi da makami, satar dabbobi, da kuma garkuwa da mutane tare da nuna alhininsa ga waɗanda lamarin ya shafa, gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya bada tallafin kuɗi Naira miliyan 38 ga iyalan mutanen da harin ƴan bindiga ya shafa a ƙananan hukumomin Musawa da Sabuwa.

Waɗanda da suka amfana da tallafin kuɗaɗen sun haɗa da mutanen da ƴan bindigar suka kashe, da mutanen da suka jikkata, da mutanen da ɓatagarin suka yi garkuwa da su, da kuma waɗanda suka yi asarar dukiyoyinsu a sakamakon harin ƴan bindigar.

Yankunansu sun haɗa da Jiƙamshi, Bakam, Tuge da wasu na cikin garin Musawa, a ƙaramar hukumar Musawa. Sai kuma mutanen Mai bakko, Dungun Mu’azu, Unguwar Leko, Damari, Unguwar Rimi, Albasu, Gazari, Mai Ganguma, Ƴar-Kaka da garin Sabuwa dake a karamar hukumar ta Sabuwa.

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Katsina kan waɗanda harin yan bindiga ya shafa da ƴan gudun hijira, Hon. Sa’idu Ibrahim Ɗanja kuma Kogunan Jibia, ya miƙa tallafin a madadin gwamnan jihar, inda a cikin jawabinsa ya jajenta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

Kogunan, ya ce Gwamna Raɗɗa ya umurce shi da ya faɗa wa sakatarorin ilimi da shugabannin
makarantun firamare da su ɗauki yaran da suka rasa iyayen su zuwa makaranta mafi kusa da su nan take domin ba su ilimin zamani kuma kada su karbi kowacce irin takarda ko kuɗi daga gare su.

Ya ƙara da cewa su kuma malaman makarantun su sanar da hukumar ilimin domin karɓar kayayyakin karatun da gwamnatin jihar ta samar wa ɗaliban da suka haɗa da littafai, kayan sawa na makaranta da sauransu.

A nasa jawabin, Sakataren ƙaramar hukumar Musawa, Hon. Ahmad Surajo wanda ya wakilci shugaban ƙaramar hukumar Musawa, Hon. Habibu Abdulƙadir, ya yaba wa ƙoƙarin gwamnatin kan yaƙi da ta’addanci, ya na mai bada tabbacin cewa ƙaramar hukumarsa za ta cigaba da bada goyon baya ga matakai da gwamnati ke ɗauka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suke addabar yankin.

Shugaban ƙaramar hukumar hukumar Sabuwa, Hon Farouk Sabuwa ya buƙaci gwamnatin jihar da ta ƙara ƙaimi domin shawo kan ƙalubalen na rashin tsaro domin samun wanzuwar zaman lafiya ga mazauna birni da karkara.

By Babaji